WANI DAN SIYASA DA YACI ZABE.

0

WANI DAN SIYASA DA YACI ZABE.
________________________________________________
Jaridar taskar labarai ta fito da wani da wannan fili don bada labaran ‘yan siyasa da suka ci zabe don yi masu hannun ka mai sanda.

A tsarin labarin ba zamu rika kawo sunan mutum ko na gari ba, amma zamu kawo halayyarsa da dabi’unsa, da mukamin da yake rike.

Rubutun riga ce maras wuya, duk wanda yake jin in ya saka za ta yi masa dai-dai ruwansa. Duk abin da zamu rubuta babu sharri a ciki tsagwaron gaskiya ne da muka tabbatar. Wannan na daga cikin tsarin Jaridar na binciken musamman da ilmantar da mutane . Rubutun zai rika fitowa da Turanci a shafin the links news. Asha karatu lafiya.

RIGA BA WUYA; WANI DAN SIYASA DA YACI ZABE.

A kwai wani dan siyasa da ya samu kujerar majalisar tarayya a Abuja, yana wakiltar kananan hukumomi biyu a jihar Katsina.

Yaci zaben fitar da gwani ne saboda da dalili biyu, na farko suruki ne. na biyu gab da zaben yazo da makullai na babura ya raba ma deliget, yace duk wanda ya zabe shi zai fadi inda baburan suke yaje ya dauko shi ma daga baya ta tabbata yaudara ce.

A zaben gari duk yasan dole gwamnati tayi amfani da karfinta don kar aji kunya, yana zangon zamansa majalisa ne karo na biyu, amma duk kananan hukumomin biyu da yake wakilta ba aikin naira miliyan biyar a tsaye wanda yayi ko wanda ya kawo aka yi daga gwamnatin Tarayya.

A majalisar tarayya bai taba kawo kuduri ba bai ma damu da zaman majalisar ba, yana kokarin zama ne don kawai ya cika dokar cewa kar dan majalisar da ya wuce lokaci kaza bai zo majalisar ba, kullum yana kasashen duniya yana ganin taswirar gidaje don ganin samfur din ginin da zai yi ya saka shi kasuwa, domin daga sana’arsa ta gina gidajen saidawa.

Ance bai iya magana na ba. Ko waka yake babu mai fahimtar me yake cewa, an zo wani taro aka ce kar ko wa yayi magana ya dage sai yayi, aka kyale shi da ya gama maganar aka rasa gane da wace Hausa yayi koda yaren kasar Chaina.

A azumin da ya wuce kowace karamar hukumar da yake wakilta abin da ya basu tallafin azumi naira dubu dari shidda da hamsina, kananan hukumomin biyu naira miliyan daya da dubu dari uku.

In zai zo ganin gida zai riko kudi na adadin kowace karamar hukuma in sun kare ko me zai faru baya kara wadansu.
Ba ruwanshi da jaje, ko ta’aziyya ba ruwansa da murna ko Allah shi Albarka ba ruwanshi da girmanka ko matsayi yace shi abin da zuciyarshi ta karanta masa shi zai aikata kuma ba canji.

Mahaifinsa da mahaifiyarshi duk suna da rai. Mahaifinsa ya na fada wa jama’a, ku bar kawo mani maganarsa don ko na bashi shawara baya dauka balle aiki da ita.

Wani halinshi yafi kowa saurin daukar waya, kuma kana gama maganarka. Amsar daya ce in har wata bukata kake nema. to kayi hakuri ba wahalar da shara’a.

Baya shiga harkar kowa kuma baya kwana da kowa a zuciyar shi in har ranka ya baci ga wasu hallayarsa ruwanka.

Yakan yi ikirarin cewa “Ni bana kwana da kowa mummunan nufi a zuciya ta, bana kullawa kowa sharri, bana shiga harkar kowa bana cutar kowa. Laifina ina aikata abin da zuciya ta ta natsu dashi inji shi”

Kun ji labarin wannan dan siyasar da yaci zabe mai rike da mukamin dan majalisar tarayya a Abuja daga jihar Katsina.

Riga ce mai wuya wanda tayi masa dai-dai ya saka babu ruwan Taskar Labarai.

Sai wani labarin a wani lokacin
________________________________________________
Kaji dadin labarin? Ziyarci shafin mu na www.taskarlabarai.com da kuma na Turanci a www.thelinksnews.com. kana da labarin da zaka bamu aika ta Whatsapp ga 07043777779 .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here