YADDA AKA KASHE SHUGABAN JAM’IYYAR APC NA BATSARI

0

YADDA AKA KASHE SHUGABAN JAM’IYYAR APC NA BATSARI.
~~~ Da abinda ya Biyo Baya

Daga Muhammad Ahmad @Taskar Labarai

Bayanin da muka samu daga majiyoyi masu tushe na kashe Abdulhamid sani shugaban APC na karamar hukumar Batsari, jahar katsina, shi ne shi dai yana shugaban na APC yana kuma cikin yan kwamitin dake sasantawa da barayi na karamar hukumar Batsari.

Ya san wadansu sun kuma san shi. A satin da ake ciki wani barawo da bai tuba ba mai suna Kwalli ya shigo Batsari, sai ‘yan banga suka kama shi suka ba ‘yansanda. Wanda aka wuce da shi Katsina. Yanzu haka yana tsare a hedkwatar yan sanda ta katsina

Bayan kama kwalli sai shugaban dabar barayin da Kwalli ke ciki wanda ake kira da suna Manu Wargaje, ya bugo ma Abdulhamid waya shugaban APC yace a matsayin shi na dan kwamitin sasantawa yana son yayi magana a sako Kwalli sai shi kuma yace magana yanzu tana wajen ‘yansanda don haka ba zai sa baki ba.

Shugaban na APC yana da wani rabon gado na ‘yan uwansa da zai yi a garin su na Dunburawa. Ana tsakar rabon gadon suka zo amma basu iske shi ba.

Sai suka sami wani informa mai suna Shamsu suka bashi kudi da lambar waya suka ce masa da ya ga Abdulhamid yazo garin ya fada masu, yau lahadi shugaban na APC yaje garin yana zuwa ya tara ‘yan uwansa aka ci gaba da maganar gado, shi kuma informa Shamsu ya kira Manu Wargaje yace gashi yazo. Wasu yan garin sunji lokacin da shamsu keyi wa su manu waya.

Su kuma su ka zo a babura guda biyu., daya Manu Wargaje shi daya dayan babur din kuma su biyu a sama.

Suna zuwa sai suka ce yazo su tafi da shi, shugaban na APC daji zasu rike shi sai an sako Dan dabar su. Kwalli shi kuma yace baya zuwa ko’ina. Nan suka fara gardama. Jama a na gefe suna kallon ikon Allah. Sai suka ce in yaki bin su sai dai su kashe shi.

Sai suka yi kokarin harbin shi bindigar taki kama shi, sai suka yi ta bugun shi, da karfe da kuma kota, suka bankare shi suka daga hammatarsa suka harba bindigar nan take ta tashi, suka barshi jinajina lokacin bai kai ga mutuwa ba daga baya ya rasu.

Nan da nan kwamitin sasanci na Batsari suka shaida ma Fulanin da aka samu fahimta dasu akan abin da ya faru. Su kuma suka ce aba su mintuna kadan zasu dau mataki.

Inda suka bi sawun Manu Wargaje da mutanen biyu suka same su a kwarin wata korama suna hutawa duk suka kashe su, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana.

Sannan suka bugo waya ga hukumomi a Batsari suka ce sun kashe su gawarwakin su tana waje kaza a je a dauko don a nuna wa duniya.

Fulanin sun ce sun dau matakan ne, don kar a tura masu sojoji suyi masu kan mai uwa da wabi.

Jama’ar gari da kuma fulanin sun shiga farautar Shamsu informa, don su kashe shi amma ya cika bujenshi da iska ya gudu.
Anyi Jana izar shugaban na APC a nan garin batsari. ta jahar katsina
_______________________________________________
Jaridar Taskar Labarai na a www.taskarlabarai.com da kuma ta Turanci ta www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta duk sako a 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here