YAN TA’ADDA SUN NACIN KARANSU BABU BABBAKA A KARAMAR HUKUMAR FASKARI JIHAR KATSINA.

0

YAN TA’ADDA SUN NACIN KARANSU BABU BABBAKA A KARAMAR HUKUMAR FASKARI JIHAR KATSINA.

Daga Awwal Jibril ‘Yankara

@ jaridar taskar labarai

Tun daga Ranar (16-4-2020) ‘Yan ta’adda ke cin karensu babu babbaka a fadin karamar Hukumar Faskari ta jihar Katsina,

Kullum garin Allah ya waye sai kaji garin da suka shiga ko su dauki mutum dan neman kudin fansa ko su kashe Mutane su kori dabbobi su. wani Lokacin su hada duka,

A ranar Alhamis 16-4-2020 su ka dauke Amarya da kawarta a Garin ‘Yankara. Juma’a 17-4-2020 suka kashe wani matashi Sunusi Ali mai sana’ar kabu-kabu kusa da garin na ‘Yankara

Asabar 18-4-2020 shiga garin Doka. Lahadi 19-4-2020 suka kashe Mutum 3 ciki har da jami’in kiyon Lafiya a kan hanyar Sabon Layin Galadima.

Litinin 20-4-2020 suka shiga Unguwar Barau suka dauki Alh Yahaiya. Talata 21-4-2020 Suka shiga garin Mabai suka kore musu Shanu da kisan kai. Ranar 22-4-2020 suka sake dawo wa ‘Yankara suka dauki ‘Ya’yan Alh Aminu kanana yara guda 3. A ranar 23-4-2020 suka shiga Ung. Sarki a ranar 24-4-2020 suka shiga Burtsatse. A ranar 25-4-2020 suka shiga Kafi, ranar 26-4-2020 kuma suka shiga Unguwar Doka. Sai kuma ranar 28-4-2020 suka shiga Unguwar Boka.

Haka dai abubuwan ke tafiya kullum sai kaji inda ‘Yan ta’addan suka shiga, kuma duk inda suka je bawani abu daga kisa sai fayde sai kore dabbobin mutane da kuma garkuwa da su, kullum aikin ke nan.

Ko a ranar 28/5/2020 da karfe 11:00 na dare, sun shiga Unguwar Gizo inda suka kashe mutum 13, suka harbi mutum 7 yanzu haka suna asibiti, sun kuma dauki mace 1 sun tafi da ita. Sun kwashe musu dabbobi gaba daya (Shanu, awaki da Tumaki).

Haka kuma, sun shiga Sabon Layin Galadima sun barke shagunan mutane sun kwashe kayan abinci da kayan masarufi.

See also  KUNGIYA A BATSARI; TA KARRAMA JAGORORIN TSARO.

Daga nan suka wuce Maigora inda suka barke shaguna suka kwashe kayan abinci da kayan masarufi kuma sun harbi wani mutum daya.

A garin Mairua kuma sun dauki mutum biyu sun harbi wani yaro. yanzu haka yana asibiti domin kula da Lafiyar sa.

Har yanzu Baturen ‘Yansanda mai kula da fadin karamar hukumar Faskari yana kwance yana Jinyar harbin da ‘Yan Ta’addan su kai mai.

Haka kuma, sun yi Sanadiyar rasa kafar kwamandan ‘Yan sakai na garin “Yankara da suka harba Malam Sa’adu Binnin Ruwa.

Zuwa yanzu Allah kadai yasan addadin mutanan da suka rasa ransu ko lafiyar Ssu a fadin karamar hukumar Faskari, wasu kuma tilas sun baro garuruwan su zuwa Matsugunan makaratun boko da ke cikin Garin Faskari da Daudawa.

Sakamakon rashin tsaro da ake fama da shi a karamar hukumar ta Faskari. Duk da yanayin halin kuci da Jama’a suke ciki sakamakon Annobar Korona Covid 19.

Ta Janibin Gwamnati kuma ta turo Sojoji tun ranar kawo harin garin ‘Yankara ranar Juma’a 15-5-2020 bayan kisan Abu Uwar Daba da Maharan suke jin afin kisanta da akawi wanda ta kitsa zata zo Masallaci Juma’a da an tada Sallah zata kira maharar suka wo hari kafin lokacin asirin ta ya tonu ‘Yan sakai suka kasheta.

Domin su bada kariya ga mutanen amman duk da haka ‘Yan Ta’addan nacin karan su babu babbaka, abin da ke ba mutane tsoro shi ne yuyuwar noma a vana a fadin Karamar hukumar ta Faskari.

Amman anji gwamnati tace zata kakkabe ‘yan ta’addan cikin kankanen lokaci. Na mu dai mu zura ido mugani.
________________________________________________
Taskar labarai na a www.taskarlabarai.com da yar uwarta ta turanci a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta . 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here