ME YASA AKA KASHE HAKIMIN YAN TUMAKI?

0

ME YASA AKA KASHE HAKIMIN YAN TUMAKI?

Binciken Taskar Labarai

Wani bincike da jaridar Taskar Labarai tayi ta gano wani dalili da marigayi hakimin ‘Yantumaki ya sa ya rasa ranshi akan shi.Alhaji Abu Atiku

Binciken mu tsakanin wasu Fulani da kuma iyalanshi, ya gano cewa Bafullatanin nan da ya taba sace mahardacin Alkura’anin nan Ahmad Suleman ana zargin yana da hann na kitsa kisan.

In za a iya tunawa, bayan sace Ahmad Suleman Bafullatanin da ake zargi wanda yake ya fito ne daga yankin Dangi ta karamar hukumar Danmusa. Daga cikin hanyoyin da aka bi don sako Malam Ahmad Suleman shi ne aka dauko mahaifiyar shi inda aka yi musayar ta da Ahmad Suleman. Kamar yadda majiyarmu ta shaida mana.

Bafullatanin ya zargi mutanen garin Dangi da cewa sune suka tona asirin mahaifiyarshi wanda a wancan lokacin har suka je garin a Ranar kasuwa sukayi harbe-harbe.

Daga nan shi wannan Bafullatanin sai ya kwashe shanunshi da mahaifiyar da dangin sa ya koma wani yanki na Zamfara, da niyyar zama.

Ance a can Zamfara inda yake son ya zauna an nemi ya kawo takardar cewa shi amintacce ne daga hakimin yankin shi.
Shi ne sai ya nemi shi hakimin ya bashi takarda shi kuma marigayin Alhaji Abu Atiku saboda tsoron me zai je ya dawo yaki bashi takardar.

Iyalan marigayin sun tabbatar mana da cewa bafullatanin ya rika kiranshi yana zagin shi yana masa barazana in har bai bashi wannan takardar ba.

Ko a ranar da aka kashe shi marigayin ya fada ma iyalanshi cewa, bafullatanin ya kira shi yana fada masa bakaken maganganu.

See also  Sun Kashe Abokinsu Domin Su Yi Tsafi Da Zuciyarsa

Binciken mu, ya tabbatar mana maharan da suka zo kisan baki ne, basu san maigarin ba, sai dai suka tambayi gidan kuma da suka je sai da suka yi garkuwa da dan shi ya nuna masu Maigarin.

Mun tabbatar sun zo da niyyar kisan mai garin ne kawai, ko da suka kashe shi, sai da suka nemi tabbatar da cewa shi ne suka kashen. Sun kashe Maigadinshi amma harbin farko da suka yi masa, na lahantarwa ne, amma da suka fito daga gidan zasu tafi sai suka ga kayan da yake sawa na yan banga ne, sai jagoran tafiyar yace tunda dan banga ne a kashe shi kawai. Shi ne sukayi masu harbi da yawa a jikinshi.

Da zasu tafi bayan sun gama ta’asarsu, sun tafi da diyar mamacin mai suna Aisha har sai da suka kai bakin korama inda wasu ‘yan uwansu ke jiransu, sai babbansu yace a kyale yarinyar ta koma tayi zaman jajen mutuwar mahaifinta.

Sun fada ma yarinyar mai suna Aisha cewa su makasa ne aka turo su don su kashe mamacin, sannan suka bata sakon cewa ta fada wa jama’a a rika adalci.

Taskar Labarai ta jiyo dalilai uku da ake danganatawa da wannan kisan gilla, amma wannan dalilin shi ne wanda yayi daidai da hatta makusan iyalan suka tabbatar mana.
________________________________________________
Taskar labarai na bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma yar uwarta turanci dake a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. Duk sako ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here