AN SACE SHUGABAN KUNGIYAR MA AIKATAN LAFIYA NA JIBIA .

0

AN SACE SHUGABAN KUNGIYAR MA AIKATAN LAFIYA NA JIBIA .
daga taskar labarai
Daren jiya, wasu suka sace shugaban kungiyar ma aikatan lafiya na karamar hukumar jibia a jahar katsina.( medical and health workers union)
Alhaji Hamza Musa mota ya baro katsina akan hanyarsa ta komawa jibia.aka tsaida shi dai dai wani waje da jami an tsaro ke tsaida mutane.ya tsaya tsammanin jami an tsaro ne, ashe barayin mutane ne. Anan suka fito dashi daga mota suka shiga dashi Daji.
Taskar labarai ta gano, inda ake tsammanin anan aka sace shi.sanannen wajen tsayawar jami an tsaro ne.koda Rana har zuwa yamma suna a wajen suna aiki.amma da dare yayi ake jin sun bar wajen sai barayin suka maye makwafinsu.
Ana zargin da ya taho,tun da ya San wurin akwai jami an tsaro ana tsaida shi ya tsaya.sai wannan mummunar kaddara ta same shi.
Ganau sun tabbatar wa da jaridar taskar labarai cewa, da safe aka ga matarsa ba kowa sai aka sanarwa yan sanda, Wanda suka zo suka dau motar.
Wani na kusa da Wanda aka sace ya tabbatar wa da taskar labarai cewa, sun Kira wayarshi da safiyar nan .kuma ta buga ba Wanda ya dauka.
……………………………………………………………………..
Ingantattun labarai sai taskar labarai a shafinta dake www.taskarlabarai.com da kuma na yar uwarta ta turanci dake a www.thelinksnews.com da sauran shafukan ta na Facebook da sauransu. Duk Kira ko sako aika ga 07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here