YADDA WANI LAUYA DA MA AIKATA KOTU SUKA YI SANADIN BADA BELIN WANI KIDNAFA
……………………Daga babbar kotun jahar katsina
Kungiyar Lauyoyi ta kasa reshen jihar Katsina karkashin jagorancin mataimakin sakataren kungiyar sun yi wani taron manema labarai kan zargin da ake na hannun daya daga cikin membansu na amsar beli ba bisa ka’ida ba. Wannan ya zama dole garemu da mu fito mu yi wa al’umma bayanin hakikanin yadda abun yake, domin al’umma su tatance gaskiyar magana game da bayanin da kungiyar lauyoyin ta kasa reshen jihar Katsina suka yi.
A ranar 9 ga watan Maris ne shekarar 2020 Magatakardar Babbar kotu mai lamba ta bakwai wadda ke karkashin jagorancin mai shari’a Baraka I. Wali hade da sauran wasu ma’aikata da lauyoyi sungabatarvda takardun zamba ga kotun wadanda suka hada da, takardar umurnij kotu da da takardar beli da kuma takardar izinin saki wadda kai tsaye take dauke izinin Mai Shari’a ta babbar kotu mai lamba ta bakwai, mai nuni da cewa a sallami wasu mutum biyu da ake zargi da aikata laifuka da ke tsare a gidan gyaran hali na jihar Katsina karkashin izinin Babban Majistire mai kula da kotu ta daya a Katsina.
Masu laifin dai na tsare ne domin jiran shawara daga Babar kotu kan tuhumar da ake masu, duba da cewa ita babbar kotun Majistire ta daya bata da hurumin yin shari’a ga wadanda ake zargin sakamakon laifukan da ake zargin sun aikata wadanda suka hada da Makirci Garkuwa da Mutane da kuma zama cikin kungiyoyin manyan barayi.
An bayyana cewa Magatakardan da sauran abokanansa sun gabatar da wasu takardun kotu na boge, wadanda ke bayar da izinin bada beli, da kuma izinin saki ga babban Mai Shari’a na jihar Katsina wanda ya yi tsamanin takardun na gaskiya ne, ya sanya masu hannu, aka gabatar da takardun babban mai kula da gidan gyaran hali na jihar Katsina, inda aka sallami wadanda ake zargin.
Babban jojin ya fahimci lamarin ne bayan da babban jami’in kula da bangaren shari’a na jiha ya shigar da korafin wadanda aka saki din sun kara aikata laifin garkuwa da mutane tare da kashe wani mutum a Mararrabar Kankara a karamar hukumar Malumfashi, bayan su kuma bangarebsu bai ma san hanyarvda aka bi wajen bayar da belin ba.
Wannan yasa babban jojin ya sa aka dauko mashi fayal din da ke kunshe da bayanin masu laifin daga babbar ma’ajiyar aje fayil-fayil na masu laifi, inda ya gano cewa takardar neman izinin bayar da belin ba a shigar da ita ba a ma’ajiyar kamar yadda aka saba. Haka kuma ya gano cewa lambar laifin KTH/198M/2020 bayanin da ke ciki na shari’a ba shi ne ainahin bayanin shari’ar wadanda aka bayar da belin nasu ba.
Haka kuma ya gano cewa takardar belin tana dauke da sanya hannun babban jami’in shari’a U.D Farouk mai aiki a jibiyar da ke bayar da lauyoyi ga mutanen da ake tuhuma da manya laifuka kuma basu da karfin daukar lauya. Haka kuma an buga ma takardar satam na Kungiyar lauyoyi ta kasa. Haka kuma lauyan da ke neman belin ya gabatar da wanda ya zai tsaya a bayar da belin, bayan da ya gabatar da takardar gabatarwa ta bohi dake da sa hannun hakimin Kankara wanda wadanda ake zargin sun fito daga yankin ne.
Wannan dabi’a da halayen da magatakardan tare da abokanan kullinsa suka nuna sun zama yaudarar shari’a da laifuffukan da suka shafi gudanar da aiki a bangaren shari’a a a karkashin sashi na 124 da 125 da 141 da kuma 148 na kundin tsarin laifula da hukuncinsu na jihar Katsina, Babban Jojin na jiha ya tura kes din ga sashen tsaro na farin kaya domin yin bincike da kuma fito da gaskiya yadda lamarin ya faru, domin daukara mataki. Ya yi karin haske da cewa, wannan ba laifi bane kadai, cin amana ne da kuma yin zagon kasa ga sha’anin tsaro na kasa, da kuma sauran lamurrana da suka shafi shari’a.
Sashen tsaro na Farin kaya sun gudanar da kwarya-kwaryan bincike, inda suka gayyaci duk wani mai ruwa da tsaki game da laifin, wanda ya hada da hakimin Kankara, wanda takardar gabatarwa ta boge ta fito daga ofishin sa. Babban jami’n da ke kula da gidan gyaran hali na jihar Katsina wanda ya sallami wadanda ake tuhumar ba tare da na gabatar da su gaban babbar kotun majistare ba domin tabbatar wa.
Haka kuma shi U. D. Farouk yayi alkawari a rubuce gaban babban jojin jiha cewa zai shirya yanda za a sake kama masu laifin da aka saki bisa yaudarar kotu, kuma hukumar DSS suka aminta da yin hakan , amma har sama da sati daya bai iya yin hakan ba. Saboda haka ne aka tsare shi, tare da gabatar da shi a gaban kotu. Lokacin da aka gabatar da bukatar bada belin ma’aikatan shari’ar tare da shi lauyan, da sauran wadanda ake tuhuma da laifin a gaban babbar kotun jiha ta 6 , sai kotun taki amincewa da bada belin su. Kungiyar lauyoyi (NBA) ta san hanyar da ake daukaka kara, amma maimakon tayi hakan, sai ta zabi ta yayata abin ga jama’a, ta hanyar kiran taron Manema labarai da ikirarin cewa U. D. Farouk bai aikata wani laifi ba zance ne kawai, domin kotu ce kawai take iya tabbatar da hakan.
Maigirma babban jojin jiha ya kafa kwamitni da zai binciki lamarin a cikin gida. Kwamitin ya kunshi Joji daya, a matsayin shugaba , Babban sakatare a maikatar shari’a, babban Magatakardar babbar kotun jiha, wakilin kwamishinan ‘yansanda, wakilin daraktan DSS na jihar Katsina, shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar Katsina ( NBA) kuma duka mambobin kwamitin nan lauyoyi ne, kuma mambobin kungiyar NBA. Ba a jima ba da kwamitin ya mika rohotonsa, kuma zuwa yanzu ana kan nazarinsa , domin daukar matakin da ya dace .
Muna tabbatarwa da jama’ a cewar babu inda muka ce wai an yaudari babban jojin jiha ne ya saki wadannan hatsabiban masu garkuwa da mutanen, kamar yanda ake yadawa a kafafen sadarwar zamani .
Rana 4th yuni, 2020
Sa hannu
Kabir shuaibu
Babban rijistara
NB . ANYI RUBUTUN DA TURANCI.JARIDAR TASKAR LABARAI SUKA FASSARA SHI ZUWA.HAUSA. DUK WANI KUSKUREN FASSARA NA SU NE.