MANSURA ISA TA KARYATA JITA-JITAR DA AKE YADAWA A KANTA
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Jarumar masanantar Kannywood Mansura ta bayyana bacin ranta dangane da jita-jitar da ake yadawa na cewa ta yi hadari kuma ta ma mutu.
Jarumar ta bayyana haka ne a wani faifan Vidiyo da ta wallafa ta shafinta na Instagram, inda ta sanarwa da magoya baya inda ta ke cewa; Labarin ba gaskiya ba ne, karya ce kawai aka kirkira.
Mansura wacce mata ce da shaharren dan Kannywood sani musa Danja, tana cikin yan fim da ke da Gidauniyar tallafawa mabukata a Nigeriya.