Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Warware Naɗin Sabon VC Ɗin Jami’ar Dutsin-Ma
Kotun ɗa’ar ma’aikata ta ƙasa (National Industrial Court) da ke Birnin Tarayya, Abuja, ta ware naɗin sabon shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma, jihar Katsina (FUDMA), Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi, da Gwamnatin Tarayya ta damƙa masa a ranar 15 ga watan Mayu, 2020 ta hannun Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu.
Matakin ya biyo bayan ƙarar da Farfesa Haruna Abdu Kaita ya gabatar a gaban kotun ta hannun lauyansa, Bello Ibrahim Esq, a ranar 4 ga watan Yuni 2020. Lauyan ya nemi kotun da ta warware naɗin sabon shugaban jami’ar sakamakon umarnin da kotun ɗa’ar ma’aikata ta bayar a baya na hana naɗa sabon shugaban jami’ar har sai an kammala shari’ar da ke gabanta mai lamba NICN/KN/29/2017 game da rikicin shugabancin jami’ar.
Jami’ar Dutsin-Ma ta kasance a cikin rikicin shugabanci na kusan tsawon shekaru huɗu. A wani rahoto da Daily Trust ta fitar, tsawon watanni shida baya, ta bayyana cewa rikicin jami’ar ya fara, kusan shekaru huɗu baya, lokacin da aka soma samin saɓani tsakanin shugaban jami’ar, Farfesa Haruna Abdu Kaita, da hukumar makarantar ƙarƙashin Dakta Marliyya Zayyan, inda ɓangarorin biyu suka zargi juna da rashin martaba juna.
Rahoton ya ce Marliyya Zayyan ta kira wani taro inda suka yanke hukuncin dakatar da Farfesa Kaita a kan zargin aikata wasu laifuka, waɗanda shi kuma ya musanta aikatawa.
A wata tattaunawa da ya yi da Daily Trust, Farfesa Kaita ya bayyana cewa ya garzaya kotu domin wanke kansa daga zargin da suka tuhumce shi da shi tare da ganin kotun ta maido da shi kan kujerarsa.
“Rikicin da muke yi ya fara ne kasancewar hankalin hukumar makarantar bai kwanta ba da ƙa’i’dojina na ganin an tabbatar da cewar an gabatar da ayyuka yadda ya dace. Wannan shi ya kawo batun dakatarwar da suka min domin cimma wasu muggan muradai.
“Zan ci gaba da bibiyar shari’ar, har sai an yi adalci, an kuma maido da ni,” Farfesan ya faɗa.
Daga baya Dakta Marliyya Zayyan ta damƙa wa Farfesa Kaita takardar sallama mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Afrilu, 2017 a kan dalilan wasu zarge-zarge da tun a baya ya musanta aikata su.
Bayan nan hukumar jami’ar ta fitar da sanarwar neman sabon shugaban jami’ar domin maye gurbin Farfesa Haruna Abdu Kaita. Ganin haka yasa kotun ɗa’ar ma’aikata ta ƙasa ta yi umarnin haramta naɗa sabon shugaban jami’a a makarantar har sai bayan ta yanke hukunci. Hakan ya sa tsawon shekaru jami’ar ta kasance ƙarƙashin mulkin muƙaddashin shugaban jami’a.
Duk da umarnin da kotun ta bayar na haramta zaɓen sabon shugaban jami’ar, kwatsam sai ga rahotanni sun fito na zaɓen Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi da Gwamnatin tarayya ta yi a ranar 15 ga watan Mayu, 2020, a matsayin sabon shugaban jami’ar. Hakan ya sa Farfesa Haruna Abdu Kaita ya kuma shigar da sabuwar ƙara a kotun ɗa’ar ma’aikata da ke Abuja.
Bayan saurarar ƙarar da lauyan mai ƙarar, Bello Ibrahim Esq, ya shigar, kotun ta bayar da umarni kamar haka:
1. Haramta naɗa Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ko wani mutum daban a matsayin shugaban Jami’ar Dutsin-Ma.
2. Haramta wa Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi shiga ofishin shugaban jami’ar, da kuma gabatar da aikin shugaban jami’ar Dutsin-Ma.
3. Haramta wa Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi kiran kanshi a matsayin shugaban jami’ar Dutsin-Ma ta kowacce irin fuska har sai kotu ta gama yanke hukunci.
Kotun ta ɗage zaman zuwa ranar 17 ga watan Yuni, 2020