‘A SHIRYE NA KE NA AMSA KIRAN KOCIN NIGERIYA IDAN AN KIRA NI’—inji Mustapha Ibrahim

0

‘A SHIRYE NA KE NA AMSA KIRAN KOCIN NIGERIYA IDAN AN KIRA NI’—inji Mustapha Ibrahim

Daga Ibrahim Hamisu

Dan wasan da ya fi kowa cin ball a primiya ta Nigeria Mustapha Ibrahim ya ce yana jiran gayyata daga babban kocin kungiyar kwallon kafa ta Nigeriya Super Eagles wato Gernot Rohr domin ya bada ta sa gudunmawa bugawa kasarsa ta haihuwa.

Mustapha Ibrahim wanda dan asalin Maiduguri ne, da ya ke taka leda a kulub din Filato united, ya ci kwallaye 11 a cikin wasa 25 da ya buga, wanda daga shi wasan ne aka tafi hutun Corona,

Kwanan nan dai hukumar ta NPFL ta sabunta wa ganet rohr kwantaragi shekara biyu, inda ya yi alkawarin baiwa yanwasa daban-daban dama da ke buga wasa a gida Nigeriya.

See also  Masari bai yi ganawar sirri da Fati Muham-mad ba – S. A. Sabo Musa

Mustapha Wanda tshon dan wasan Elkanemi warriors da Eyemba ne, ya halacci gasar kwararrun Afirka mai suna CHAN a sherar 2018.

Ya ce “Nigeriya tana da kwararrun kuma gogaggun yan wasa ni ma zan iya sa kaina a cikinsu, dama ce mai muhimman da mai horaswa ya kamata ya baiwa yan wasanmu na gida,

“Ina da tabbaci idan aka bani dama zan goga kafadata da yan wasan da ke bugawa a turai, nasan suna da gogewa, amma ina da tabbacin zan yi aiki tukuru don na baiwa mara da kunya”.inji Mustapha Ibrahim.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here