Gwamna Ganduje ya raba gidaje 200 kyauta ga Fulani

0

Gwamna Ganduje ya raba gidaje 200 kyauta ga Fulani

Daga Ibrahim Hamisu

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya jagoranci kaddamar da rabon gidaje kyauta domin inganta harkokin kiwo da rayuwar fulani makiyaya a fadin Jihar Kano, wanda aka gabatar a dajin Dansoshiya dake karamar hukumar Kiru karkashin kwamitin duba wajen tabbatar da RUGA da kasuwar Nono karkashin Dr Jibrilla Muhammad.

Gwamna Ganduje ya ce kasancewar sa Bafulatani Makiyayi kafin kasancewar sa Gwamnan, ya zama lallai ya tallafawa makiyayan wanda hakan zai inganta rayuwar su data yayansu.

A yau an fara rabon gidaje 25 da aka kammala daga cikin gidaje 200 wanda Gwamnatin zata gina a wannan daji Sannan anyi rijiyoyin butsatse don shan ruwan shanunsu a gurare 5 cikin dajin tare da aikin gina dam wanda aikinsa ya tsaya saboda damina.

Cikin abubuwan da za a gina a wannan daji sun hada da makaranta da asibitocin mutane da na dabbobi domin inganta rayuwar su da magance rigingimun makiyaya da masu satar shanu.

Gwamna Ganjuje ya samu rakiyar Mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna, Kwamishinonin Ruwa, Ilimi, Yada Labarai, Daraktan Tsaro na Fadar Gwamnati Col Umar Malami da sauransu

   

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here