MUTUM 12 SUN HARBU DA KORONA A KANO

0

MUTUM 12 SUN HARBU DA KORONA A KANO

Daga Ibrahim Hamisu

Maaikatar lafiya ta jihar Kano ta bayyana a shafinta na Tiweta cewa a yau asabar da karfe 11:45, ta ce mutane 52 ne aka yi wa gwajin cutar Korona a jihar,

Mutum 12 daga ciki an tabbatar suna dauke da cutar, yayin da aka sallami mutane 33 bayan sun warke ragas,

Sannan kuma mutum 2 sun rigamu gidan gaskiya tanadiyyar wannan annoba ta Korona Virus.

Don haka jimillar wadanda aka gwada sunkai 5,347, sai jimillar wadanda suka harbu da cutar 999, sai wadanda a halin yanzu suke da cutar 536, wadanda aka sallama kuwa sunkai 415, sai kuma wadanda suka mutu adadinsu ya kai 48.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here