AN DAKATAR DA DALIBAR DA TA KALUBALANCI GWAMNATIN JIHAR NASARAWA

0

AN DAKATAR DA DALIBAR DA TA KALUBALANCI GWAMNATIN JIHAR NASARAWA

Gwamnatin jihar Nasarawa ta umarci shugaban Makarantar koyarda aikin kula da majinyata da Ungwan zoma ta birnin Lafiya Mr. Zari Solomon da ya dakatar da Ɗalibar Makarantar Zulaihat Ibrahim Doma na tsawon shekara guda bayan an sakata ta rubuta wasikar tuba a shafin sadarwar ta na Facebook.

Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, wannan yarinya dai dalibace a bangaren koyan aikin Ngozoma, Laifinta Shi ne ta kalubalanci Gwamnatin jihar Nasarawa kan yadda tayi watsi da makarantar da take ciki a ranar 18 ga watan Afrilun Shekarar 2020.

An yi mata wannan hukunci ne A yau 9 ga Watan Yunin 2020, saboda faɗan gaskiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here