MAHAIFIN FITACCEN JARIRIMI ALI NUHU YA RASU

0

MAHAIFIN FITACCEN JARIRIMI ALI NUHU YA RASU

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

A yau Litinin, 8 ga Yuni, 2020, da yamma nan, Allah ya yi wa mahaifin fitaccen jarumi Ali Nuhu rasuwa.

Mista Nuhu Poloma ya rasu a Gombe sakamakon gajiyar rashin lafiya da ya yi,
Iyalin sa sun faɗa wa mujallar Fim cewa shekarun sa 79 a duniya.

Mista Poloma tsohon ma’aikaci ne a hukumar Kwastam ta Nijeriya, sannan ya taɓa zama ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Tangale da Waja a Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar NPN kafin a ba Gombe jiha.

Bugu da ƙari, ya taɓa zama shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Gombe, cikin ‘ya’yan sa akwai Kiristoci da Musulmi, ya auri mahaifiyar Ali Nuhu, Hajiya Fatima, a Kano, Wanda dama ita ta jima da rasuwa.

Muna add’uar Allah ya ba jarumi Ali Nuhu da ‘yan’uwan sa haƙurin rashin mahaifin su, amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here