Majiyar taskar labarai a hukumar EFCC sun tabbatar mana cewa Alhaji idi kwado sarkin aikin katsina, Wanda hukumar ta kama kwanakin baya a wani kwantar bauna da bibiya da sukayi masa a katsina.
Yana baiwa hukumar hadin kai sosai. Majiyarmu tace ya zuwa jiya Talata ya cika takardu da yawa kuma duk ya Sanya masu hannu.
Majiyarmu tace, duk abin da ya sani baya wata gardama zai tabbatar kuma yayi bayanin me ya faru.da yadda abin yake.
Majiyarmu tace , ya bayyana wa hukumar cewa tsoron me za ai masa ya Sanya yaki yarda a kama shi.amma ba Wanda yace masa wai ya gudu ya boye.kamar yadda ake zargi.
Hukumar sun ce, samun idi kwado ya Sanya masu wani sabon lale a hujjojin da suke dashi na gabatar da jami an tsohuwar gwamnatin shema da akeyi.akan wasu badakar kwangiloli.
Majiyarmu a hukumar tace, shara ar shema na iya shiga wata sabuwar gwamnatin da , zai zama kila jama ar katsina zasu iya gani wani zamani na kallo da jin Shari o i , biyu na gwamnatin daban daban a jaha daya.
Majiyarmu tace, EFCC na da takardun koke daban daban, Wanda ba za su fara binciken su ba. Sai gwamnatin dake sama ta dauka. Don haka Al adarsu take. @ jaridar taskar labarai www.taskarlabarai.com