AN SAMU KARIN MUTUM 16 DA CUTAR KORONA A KANO
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Maaikatar lafiya ta sanar da samun mutum 16 masu dauke da cutar Korona wato Covid-19 a Jihar Kano.
Wannan ta sa adadin wanda suka kamu da cutar a jihar Kano yanzu ya kama mutum 1020, sannan kuma mutum 50 daga ciki sun rasu sannan mutum 497 sun warke kuma an sallame su.