HAFSAT IDRIS TA JA HANKALIN MAGOYA BAYANTA
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Jaruma a masanaartar Kannywood Hafsat Idris ta gargadi magoya bayanta cewa su yi hattara, domin duk wanda ya yi masu magana a shafin facebook mai suna Hafsat Idris to ba ita ba ce, dan damfara ne da ke amfani da shafin na ta na facebook,
Jarumar ta bayyana haka ne a wani faifan Vidiyo da ta wallafa a shafukan sada zumunta, ta kuma kara da cewa da zarar ta wallafa sako a shafinta na Instagram sai su kwafa su wallafa a shafin na facebook,
Hafsat Idris ko ka ce Hafsat Barauniya, yar unguwar Gadankaya ce da ke cikin birnin Kano, tauraruwarta na haskawa tun lokacin da ta shiga masanarta a shekarar 2015, inda ta fara da Fim mai suna Barauniya.