HARI DA KISAN GILLAR KADISAU AKWAI MAKARKASHIYA A CIKI

0

HARI DA KISAN GILLAR KADISAU AKWAI MAKARKASHIYA A CIKI

Binciken Taskar Labarai

Wani hari da mahara suka kai a garin Kadisau karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina wanda ya haddasa mutuwar mutane da yawa, taskar labarai ta gano akwai makarkashiya da wani shiri boyayye a cikin mummunan ta’addacin da aka yi.

Binciken mu ya gano wadanda suka kai harin kwararrun mayaka ne, masu horo irin na soja ba kamar irin Fulanin da aka saba gani ba wadanda ke harba bindiga barkatai.

Wasu ganau da suka tsira da ransu sun fada mana cewa yadda maharan ke harbi da yadda suka rika sabkowa a bisa babura da yadda suka rika bin mutane da ga ni kasan kwararru ne ba ‘yan ta more ba. Gasu rike da abin magana kamar woki toki ..inji wasu da suka tsira da kyar.

Wadanda suka tsira da kyar sun shaida mana cewa, dukkaninsu sun shafa irin shuni a fuskarsu kuma basa magana ko kiran suna sai dai bada umurni da hannu da kuma tsawa.
Wanda in fulani ne, zaka ji suna Hari suna magana da Raha da dariya da umurni a fulatanci.

“yadda suke tafiya kamar yadda na ga mayaka na yi a finafinan yaki” ne “”, inji wani da ya shaida wa jaridar nan.

Kauyukan da ke kusa da garin sun fada mana cewa anyi kwanaki in da suka lura wasu mutane na ta kewayen kauyukan nasu kamar suna binciken wani abu.
Kuma suna nazarin kowane kauye Kafin su wuce wani.amma basu shaida jami an tsaro ba.sai dai an gansu rukunin uku uku suna yawo a ikirarin wani da fada mana

“Yadda suka rika harbi don kisa da kuma yadda suka shiga kone-kone da gani sun zo ne da niyyar yin barna mummuna yadda zai jawo hankalin duniya akan abin da suka yi” inji wani da ya tsira yana fada wa jaridar nan.
Hatta yadda manyan gidajen rediyon duniya suka dauka yan awowi da faruwar abin, yayi kama da wani ya rika buga waya yana basu labarin abin da faru kila da tabbatar masu cewa an kai Hari da mummunan kisa.abin ya fi kama da tsararre abu. Kamar yadda muka fahimce shi.da sanin yadda labarai irin wannan ke yaduwa.

Duk wadanda suke da masaniya akan yadda Fulani tsantsa ke kai hare-harensu mafi yawa sun fi kaiwa da dare ko in duhu yayi, kuma mafi yawan inda suke kisa na rashin imani sai in zasu dau fansa.ko akwa wata azazza.

Wannan harin da rana suka kai, kuma garin bai da wani tarihi na tsama da Fulani, illa kawai gari ne masu kiwo kuma suna da dabbobi sosai.

“Da suka shigo fashewa akai garin, inda sata ta kawo su sai suyi satar su fita, amma suka kashe suka kone sannan suka kora masu dabbob” inji wani dan garin da ya tsira.

Bayanan da jaridar nan ta tara ta gano harin nan akwai wani makircin da makarkashiya wanda bincike ne zai bankado gaskiyar yadda yake.

Bayan harin jami’an tsaro sun cika garin wanda ya bada damar aka yi Jana’izar wadanda aka kashe da yawa suna jinya a asibitoci da gidajen dangi.
________________________________________________
Taskar Labarai na a bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma ‘yar uwarta turanci a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. Duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here