SABUWAR FASAHAR DUBA MARASA LAFIYA DAGA GIDA

0

SABUWAR FASAHAR DUBA MARASA LAFIYA DAGA GIDA

Daga Ibrahin Hamisu, Kano

Shugaban Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe, yayi kira da al’umma dasu yi amfani da sabuwar fasahar duba marasa lafiya daga gida, da asibitin ya kirkiro, a dai dai lokacin da al’umma ke bin dokar zaman gida dole.

Yaci gaba da cewa, la’akari da yawaitar marasa lafiya a dai dai wannan lokaci, wannan sabuwar hanyar duba marasa lafiya, zata taimaka matuka wajen dakile yaduwar cutar coronavirus, a tsakanin al’umma.

Sannan shugaban ya nuna damuwarsa, kan yadda Al’umma musamman mata na wannan yanki ke yin burus da wannan babbar dama, inda alkaluma ke nuna al’ummar da ke nesa sunfi amfana da wannan sabuwar hanya,

See also  FIXING THE ACCESS ROAD TO THE FEDERAL UNIVERSITY OF TECHNOLOGY, OWERRI, IMO STATE!

Da yake Karin bayani, shugaban sashen kirkiro da sabuwar fasahar, Mr.  Onunze Ifeany, yace za’a ci gaba da amfani da sabuwar fasahar wajen duba marasa lafiya, har ya zuwa karshen annobar corona.

Ya ci gaba da cewa, sabuwar fasahar, ita duniya ke tafiya akai a dai-dai wannan lokaci.

Dr. Fatima Abbas, likita a sashen duba iyali na asibitin, tace marasa lafiya daga ko’ina a kasar nan zasu iya kiran wannan lambar waya 018885014, don samun damar duba su daga gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here