BA MU DA WAKILCIN DAN MAJALISSAR JIHA A KARAMAR HUKUMAR RIMI: SHEKAR BIYAR NA MULKIN APC

0

BA MU DA WAKILCIN DAN MAJALISSAR JIHA A KARAMAR HUKUMAR RIMI: SHEKAR BIYAR NA MULKIN APC

Daga Abu Amir

Kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 sashe na biyar bangare na biyu shi ya bayar da dama ga kowace karamar hukuma ta mallaki Danmajalissa da zai wakilce ta a jiha domin zartar da doka da kuma gabatar da korafe-korafe na mutanen karamar hukuma ga gwamnatin jiha. Kundin ya kawo tsari da kuma hanyoyin da ya kamata a zabi Danmajalisar jihar ko kuma a mayar da shi gida in ana ganin zabin da aka yi mashi bai gamsar ba, ko kuma ya gaza aiwatar da aikin da aka tura shi.

A gefe guda kuma akwai wasu lalurori da ka sanya Karamar hukuma ta rasa wakilici a jiha, kamar yadda karamar hukumar Rimi ta rasa.

Irin wadannan lalurorin sun hada da rashin lafiya wadda zata kwantar da wakilin ko kuma tsarewa a karakashin ikon kotu kafin a tabbatar da aikata laifi ko akasin haka. Sai kaso na uku wanda shi ne ya shafi Rimi, wato rashin bin kadi da kin sauraren wadanda kake wakilta tare da nuna kyashi ko hassada akan duk wani abun cigaba da ya samu karamar hukuma, sakamakon gazawa da Danmajalissar ya yi na aiwatar da ayyukansa yadda ya kamata.

A Karamar hukumar Rimi babu wakilci a majalissar jiha a aikace sai dai wakilci a hoto, akwai dalilai da yawa da zasu iya tabbatar da haka, musamman irin koma baya da karamar hukumar ta samu a kasa da shekaru biyar na wakilcin Danmajalissar.

Akwai abubuwa guda uku da zan magana a kansu a wanann rubutun na farko, abubuwan sun hada da:

1. Rashin sauraren wadanda ake wakilta
2. Rashin bin kadin ayyuka da kawar da kai kan cigaban karamar hukumar
3. Rashin karabar shawara da kokarin hana al’ummar yankin fadar albarkacin bakinsu, tare da nuna isa da na iya.

1. Danmajalissa mai wakiltar karamar hukumar Rimi ko shakka babu yana da raunin rashin sauraren wadanda yake wakilta, baya daga wayar mutane in an kira shi in an rubuta masa wasika budadda ko rufaffa baya dibawa, akwai misalai da yawa akan haka kuma shi ma ya sani. Bayan kuma kundin tsarin mulki na 1999 Sashe na biyar bangare na biyu ya tabbatar da cewa sauraren korafe-korafen al’umma da gabatar da su na daya daga cikin aiki da kuma dalilan da ya sanya aka samar da majalissar.

Ni kaina na sha rubuta wa dan majalissar korafi da kuma shawarwari kan wasu bukatau na al’umar da yake wakilta, haka kuma ko a cikin satin nan shugaban asibitin gwamnatin jiha da ke karamar hukumar Rimi, ya bayyana a rubuce cewar ya kira danmajalissar ya fi a kirga domin ya bayyana mashi halin da asibitin ke ciki bai dauka ba.

Ina ba wannan Danmajalissa shawarar da ya gyara ya rika amsar koken al’ummarsa domin tabbatuwar ingancin wakilcinsa.

Ko shaka babu ga duk wanda ke wakiltar karamar hukumar Rimi, ya san cewa wannan Danmajalissa bai fahimci aikin majalissa ba, domin a cikin surutansa da yayi kwanakin baya a zantawar da ya yi da manema labarai ya bayyana cewa, wai ya kai koken gyara asibitin Rimi da kuma kudirin samar da Makarantar kwana da kudirin wanzar da ruwan sha a karamar hukumar Rimi, wanda duk wadannan surutai da ya yi, bai kamata ya fade su ba duba da cewa mutanen karamar hukumar Rimi masu ilimi ne kuma kwararru a fannin da ya shafi bincike da sanin yadda ake aiwatar da ayyuka a majalissun jiha da tarayya baki daya.

Kamar yadda kace ka kai kudiri da koke, amma har yanzu ba a zartar ba, wannan ya tabbatar mana da rashin sanin aikinka a fili domin Kundin tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 Sashe na biyar bangare na biyu lamba ta 100 sakin layi na biyu, ya bayyana cewa idan kaso biyu cikin uku na mambobin majalissa suka amince da kudiri kuma aka sanya masa hannun aka aikawa gwamnan domin zartarwa, to wajibi ne wadannan ‘yan majalissar su nada kwamitin wanda zai bibiyi aikin da kuma ganin an zartar da shi yadda ya kamata, idan har/aka samu kwana talatin basu samu wani rahoton ba’asin gudanar da aikin ba.

See also  PDP ta rusa kwamitin zartarwa na jihar Katsina

Shin Danmajalissa na karamar hukumar Rimi duk wadannan kudurorin da korafin da ka kai sun samu wannan ka’ida? Ta amincewar kashi biyu bisa uku na majalissa da kuma kafa kwamiti domin bibiyar ayyukan? Idan amasar ita ce e, to ko shakka babu wannan kadai ya isa al’ummar Rimi su yi ma kiranye saboda gazawa da nakasu wajen tabbatar masu da ayyukan da suke da hakki a wajenka. In kuwa amsar ita ce a’a to ina mai tabbatar ma ka koma ka sake sabunta korafe-korafen da kudurorin ka kuma bibiyi sahihiyar hanyar da ya kamata a aiwatar mana da wadannan ayyuka domin muna kishirwarsu a karamar hukumarmu ta Rimi, kuma rashin kwarewarka ta bayyana a fili.

3. Ko shakka babu Ranka ya dade Danmajalissa baka karbar shawarar mutanen ka musamman waje yin maganganu da basu dace ba akan wasu mutane da suke da gurin taimakawa al’ummar, a matsayinka na danmajalissa ba fada bane gabanka, abin da ya kamace ka zama babba kamar yadda Allah ya dora maka girman, kaji kaki jika gani kaki gani. Koda ba zaka iya taimako ba kamar yadda kake nuna wa shi taimako ganin dama ne kai ba wannan aikin aka tura ka ba.

Amma kuma shi kundin tsarin mulkin na 1999 sashe na biyar bangare na biyu lamba ta 111 ya tabbatar mana da cewa, kowane Mamba na danmajalissar jiha, zai karbi albashi da alawus da wasu kudaden shiga hade da wasu kudin kwamishin in bukatar hakan ta taso.

In ka cire albashin ka da alawus-alawus din sauran kudin ana bayar da su ne domin yin ayyukan mazabu da kuma kyautatawa al’ummarka. Tsakani da Allah ranka ya dade me al’ummar Rimi ta amfana da shi daga wadannan kudaden da ake bayar wa? Ko kuwa mu a Rimi har yanzu bukatar bayar irin wadannan kudaden bata taso ba ko bata samu ba?

Haka kuma in muka koma bangaren alakarka da jam’iyyar APC a karamar hukumar Rimi ka yi bayanin cewa kai kalau kake da kowa, amma a zahiri ba haka bane, domin adawarka yanzu a cikin jam’iyya take ba waje ba. Shin me ya kawo haka? Wannan bai rasa nasaba da watsi da kayi da mutanen da ka samu a cikin jam’iyyar wanda ka mayar da su shanuwar ware, har ta kai ga an samu bulluwar APC akida a karamar hukumar Rimi.

Ina mai baka shawara da ka dawo ka gyara mu’amullarka da wadannan mutane, wata kila ta dalilim haka matsalar ta dinke Rimi ta kai ga ci kamar yadda muke fata.

Ranka ya dade ka sani bayar da kudi ga ‘yan media domin yi maka farfaganda ba shi ne abin da ya kamace ka ba, aikin ka da kuma kwazonka shi ne zaisa ka zauna lafiya da kowa, in har kana aikin da ya dace ba sai ka bani kudi ba kace ya tallata ka aikinka ne zai tallataka. Ni ina ganin da ka dauko kudi ka ba wani domin kareka a media ko yi maka bambadanci zai fi kyau ka dauki ma’aikatan wucin gadi a asibitin koda mutum biyu ne domin taimakawa al’ummarka.

Ranka ya dade duk wannan dogon rubutun da muke tsakaninmu da kai ba muna yi bane domin bata ka ko cin mutumcinka, muna yi ne domin dukanmu ‘yan Rimi ne kuma muna bukatar a gyara fatan mu ka yi mana karin haske inda kake ganin mun yi ba daidai ba ko kuma mun fadi abin da ba haka ba ne, domin ko munki ko munso kai janabi biyu ne a wajenmu gaka wakilinmu gaka yayanmu.

Daga karshe muna tunatar da kai cewa, kundin tsarin mulki na 1999 sashe na biyar bangare biyu ya bamu zabin yi ma kiranye da kashi daya na bisa uku wadanda suka zabe ka in har suka aminta.

Muna fatan ka gyara kurakuranka in kana da su in kuma muke bisa kuskure muna fatan ka sanar da mu domin gayarawa, da kuma fahimtarka.

Allah yanyi mana jagoranci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here