HAR YANZU NI DAN PDP NE’—inji Yakubu Muhammad

0

‘HAR YANZU NI DAN PDP NE’—inji Yakubu Muhammad

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Fitaccen Jarumi, mawaki, mai shiryawa kuma mai Rubutawa a masana’antar Kannywood Yakubu Muhammad, ya bayyana cewa har gobe yana cikin jam’iyyar PDP,

Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar BBC a shafinta na instagram Larabar da ta gabata, jarumin ya ce tun da ya fara siyasa Jamiyyar PDP ya ke goyon baya, kuma har yanzu yana tare da ita,

Yakubu muhammad ya ce ba shi da ubangida a Kannywood shi ne ubangidan kansa, amma ya na da abokan arziki, duk amintaka da shakuwa da ake ganin a tsakaninsu da sani Danja, Ya ce Ibrahim Mandawari ne ya fi birgeshi a harkar Fim baki daya.

See also  2023: Tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa, Gumel ya koma PDP

Yakubu baya ga dimbin Finafinan Hausa da ya yi, ya fito a finafinan Ingilishi a kalla guda 40.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here