HARIN ‘YAN BINDIGA A BATSARI.

0

HARIN ‘YAN BINDIGA A BATSARI.
~~~~Sun yi garkuwa da mutane, sun sace dukiyoyi

Muhammad Ahmad @ taskar labarai
A ranar juma’a 12-06-2020 da rana tsaka ‘yan bindiga suka harbi wani mutum Alhaji Ibrahim a gonar shi dake Zamfarawar Madogara, sannan kuma sun tare hanyar Dan Geza sun kwaci babura guda biyu.

Haka kuma da yammacin ranar sun yi garkuwa da wani Mallamin Makaranta Hafizu Ado (Wanda da ne ga Magaji Batsari) a gonar shi dake kauyen Bakon Zabo.

Cikin dare kuma sun kai hari kauyukan Batsarin-Alhaji da Dan Tudu, inda sukayi harbe-harbe Kuma suka sace shanu da babura.

Da misalin karfe 1:45am na dare sun kai hari kauyen Saki Jiki (Bakin gulbi) inda suka yi garkuwa da mutum biyu, Alhaji Ya’u Jari Mai Masara da Da’u Muhammad. Da suka shiga kauyen sun sare kofar shiga gidan sannan suka kutsa kai ciki suka amshe duk kudaden dake hannun shi da na matan sa, sannan suka iza keyar babbar matar sa gaba ta nuna masu gidan Da’u wanda shima suka hada da shi suka yi awon gaba da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here