SHAWARA GA GWAMNATIN KATSINA AKAN HARKAR TSARO.
daga injiniya Nura khalil
1. Na farko, Mai girma Gwamna ya rushe Kwamitin Tsaro da Sasanci na Jiha cikin gaggawa;
2. Na biyu, Mai girma Gwamna ya kafa Kwamiti ya binciki yadda rusasshen Kwamiti ya gudanar da ayyukan shi,
da yadda ya kashe kudaden da ake basu na wata wata, da kuma nasarori ko rashin nasarorin da suka samu;
3. Na ukku, ya nada mai bashi shawara akan tsaro na musamman. Abu mafi a’ala ya samo wani tsohon ma’aikacin DSS dan asalin jihar Katsina;
4. Na hudu, ya nada wani tsohon Joji ya shugabanci Kwamitin bincike na rusasshen Kwamiti, sannan sabon mai bashi shawara na musamman a matsayin sakatare na Kwamiti.
5. Na biyar, ya nada sabon Kwamiti karkashin jagorancin manyan hafsoshin soja irin su Gen. Ahmad Daku da membobi daga hafsoshin soja na kasa, sama da ‘yan sanda, DSS, NIA, DMI, FCID ‘yan asalin jihar Katsina suyi aiki tare. A sa wakilai daga Emirate Council domin suke zaune cikin mutane, kuma masu ungunninsu sun san komai dake kaiwa da kowa, sannan a nada Sakataren kwamiti daga Cabinet Office.
6. Na shidda, aba Kwamiti damar dazai binciko musabbabin dalilin wannan matsala ta banditry, kidnapping, cattle rustling da yadda za’a shawo kan al’amarin.
7. Na bakwai, idan Kwamiti ya gama tsare tsaren shi, Mai girma Gwamna ya jagorance su, su tafi Abuja su kaima Shugaban kasa.
8. Idan Allah Ya sa gwamnatin tarayya, ta dauki mataki, to falillahil hamdu. Idan kuma bata yi komai ba, to sai gwamnati tai designing ta kuma gaya ma duniya dalili. Wannan shine hanyar kubuta har ga Allah wurin Mai girma Gwamna.
Nasan Mai girma Gwamna yasan matsayin rai na dan Adam a wajen Allah da kuma abunda ke abkuwa a kasashen da ake zubda jinin musulmi da wanda ma ba musulmi ba. Wallahi, summa tallahi gara Mai girma Gwamna ka rasa kujerar ka, domin ka koma Allah a yawan shekarun ka, da Allah Yai maka hisabi akan rayuka da dukiyoyin al’umma da ake asara. Kare rayukan nan da dukiyoyin al’umma yana daga farkon abunda ka rantse da alqur’ani mai tsarki a bainin mutane da aljannu da mala’ikai.
In kunne yaji, to jiki ya tsira. Wannan dai shawara ce, amma hausawa na cewa, samu dai yafi iyawa, wai hawan dokin dan maciji.
A karshe, ina bamu shawara, mu al’ummar jihar Katsina, mazan mu da matan mu, yara da manya, mu dukufa da addu’a a matsayin mu na musulmai nagari, kuma masu tsoron Allah, domin Ya fidda Gwamna Aminu Bello Masari, sauran Gwamnoni da kuma Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari daga tuggu, da dabaibayi, mallaka, da danniya daga sharrin sihiri, sammu, jifa, asiri, baki, idanu da kulumboton munafukan makusantan su, da makiya da ‘yan adawa, da masu bada gurguwar shawara, da mugayen abokai da ‘yan’uwa, da ‘yan jari hujja kuma da mugayen bokaye da ‘yan tsibbu, da ‘yan duk wanda inna ta aure baba, da malaman karshen zamani kuma ‘yan yaudara da ci da addini.
Allah Ya ganar dasu abunda ya kamata su gani, Ya jiyar dasu abunda ya kamata su ji, Ya kuma ganar dasu abunda ya kamata su gane, Ya kuma azamar da ruhin su da karfin Shi domin Shine mai karfi alfarmar fiyayyen talikai Annabi Muhammadu S.A.W, alfarmar hasken alqur’ani kuma albarkacin sunayen Shi tsarkakakku. Amin Ya Hayyu Ya Qayyum, Ya zal jalali wal Ikram, Ya Arrahmar Rahimin Ya Rabbil alamin.