MATAIMAKIN SHUGABAN JAMI’AR BAYERO TA KANO YA YA RASU (DVC Admin)
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Allah ya yi wa mataimakin-mataimakin shugaban babbar jami’ar Bayero, ɓangaren sha’anin mulki, Farfesa Haruna Wakili Haruna rasuwa, a babban Asibitin kasa da ke Abuja,
Magatakardar Jamiar Bayero Hajiya Fatima Binta Muhamnad ce ta sanar da rasuwar malamin a yau Asabar bayan fama da rashin lafiya.
Kafin rasuwarsa, ya kasance tsohon Darakta a cibiyar Dimokradiyya ta Malam Aminu Kano da ke gidan Mumbayya da ke Gwammja, haka kuma shi ne tsohon kwamishinan Ilimi a jihar Jigawa.
Ya na daga cikin ‘yan kwamitin da suka gabatar da kirkirar jami’ar Sule Lamido ta Kafin Hausa da kuma jami’ar tarayya ta FUD duk na jihar Jigawa,
Muna Addu’ar Allah ya kyautata makwancinsa Amin.