GODIYA DA BAN GAJIYA

0

GODIYA DA BAN GAJIYA

Salam, yau na kammala kwanaki shidda cur ina zaman amsar gaisuwar mahaifiyata da Allah yayi mata rasuwa kwana bakwai da suka gabata.

Ina godiya ga duk wadanda suka samu damar zuwa, da wadanda suka turo wakilai da wadanda suka bugo mani waya da wadanda suka rubuto sako. Allah ya saka da Alheri.

Ina godiya da bangajiya, ga ‘yan uwa da aminan arziki wadanda suka zo daga wasu garuruwa da jihohinsu. Allah ya biya kuma ya bar zumunci.

Ba zai yiyu a rubutu irin wannan,in jero sunan kowa ba,amma dai na san duk wanda ya mutunta daraja ta. Na sani, kuma zan rubuta in aje a inda zan rika tunawa akai-akai( don wata rana).

Wannan rashi ya sanya dole in sake lale ga rayuwa ta da mu’amalata, har zuwa lokacin zuwan tamu, Allah ya sanya muyi ta a sa’a.

Ina addu’ar duk wanda mahaifanshi suka rasu Allah ya jikansu, wanda kuma suke raye Allah ya sanya ya gama dasu lafiya. Allah ka baiwa kowane DA ikon yin biyayya ga mahaifanshi, har su Rabu lafiya. Ameen

Na gode Allah ya saka da Alheri. Allah ya bar zumunci.¥¥¥¥¥
Naku, Danjuma.08035904408###

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here