SADIQ SANI SADIQ YA JA HANKALIN MASU DAMFARA DA SUNANSA

0

SADIQ SANI SADIQ YA JA HANKALIN MASU DAMFARA DA SUNANSA

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Jarumi a masanartar Kannywood Sadiq Sani Sadiq ya gargadi magoya bayansa da kuma masoya game da wani sabon shafi na dandalin sadarwa na facebook da aka bude mai dauke da sunansa, wanda ya ke dauke da mabiya dubu goma sha shida 16,000 da ake amfani da shi wajen damfarar jama’a.

Jarumin ya bayyana haka ne ta cikin wani sako da ya wallafa ta cikin shafinsa na sada zumunta, inda ya wallafa hotan sa na asali da na karya, domin nutane su bambance tsakanin na gaskiyar da na karya.

See also  Jarumar Nollywood Halima Abubakar ta bar harkar fim

Sadiq ya sanar da magoya bayansa cewa, asalin shafin na sa yana dauke da mutane a kalla dari biyar 5000 ne.

Sannan ya ja hankalin jama’a cewa, akwai bukatar su kiyaye, don gujewa aikin ‘yan damfara da suka ya waita a shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here