CIN DANWAKE, BURODI DA GURASA NA ‘KARA KUZARIN DA NAMIJI

0

CIN DANWAKE, BURODI DA GURASA NA ‘KARA KUZARIN DA NAMIJI_Bincike

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Wata Likita mai suna Matilda Steiner-Asiedu ta yi kira ga maza da su rika cin abinci dake dauke da sinadarin ‘Iron’ cewa rashin shi na rage karfin mazakutan namiji da kan rage jindadi wajen saduwa da uwargida.

Iron sinadarin ne dake kara jini da karfi a jikin mutum.

Likitoci sun ce mutum zai yi fama da karancin jini a jikinsa idan har babu wannan sinadari na Iron a jikinsa.

Alamun rashin jini sun hada da rashin karfi a jiki, kumburin jiki, suma, tafin hannu da kafafun mutum yayi haske fat da sauran su.

Matilda ta ce banda kara karfi da jini da sinadarin Iron ke yi sinadarin na kara wa namiji karfi mazakutan sa sannan yana taimaka wa wajen samar da maniyi a jikin namiji.

See also  BINCIKE NA MUSAMMAN

Likitan ta yi kira ga maza musamman masu aure da su rika cin abincin dake dauke da sinadari iron domin samun karfi da yawan maniyi da kuzari.

Abincin dake dauke da sinadarin iron sun hada da

1. Waken soya.

2. Wake.

3. Ganyan kamar su alaiyaho, da sauransu.

4. Naman sa.

5. Naman kaza.

6. Gasashhen dankalin Hausa da na turai

7. Burodi, musamman mai laushin gaske

8. Alkama, tuwon sa ko gurasa, da danwake.

Daily Trust ta wallafa rahotan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here