RANAR ZAWARAWA TA DUNIYA

0

RANAR ZAWARAWA TA DUNIYA

Daga Ibrahim Hamisu

A yau 23 ga watan Yuli Ranar ce da majalisar dinki duniya ta ware domin tunawa da matan da mazajensu suka mutu ta duniya, a wannan rana dai ana so a sanya kulawa da lura da halin da mata suke ciki, da nufin lalube hanyar magagance ta.

Mariya Inuwa Durimin iya ta yi bayani a takaice akan rayuwar Bazawar a cikin littafinta mai suna Rayuwar Mace; daga haihuwa zuwa tsufa. Ta fara da maanar zawarcin shi kansa:

Zawarci wani yanayi ne da ya ke samun mace a yayin da ta yi aure suka rabu da mijin, ko ta dalilin mutuwa ko saki, a sakamakon haka sai a rinka kiranta bazawara.

Rayuwar zawarci tana ciki da hadari da kalubale mai yawa, macen da mijinta ya rasu takan samu saukin tsangwama daga Al’umma. Sabanin wacce sakin aure ya raba ta da mijinta takan rasa kulawa, domin kuwa hatta iyaye ba kowa ne yake cigaba da dauka da dawainiyar ta ba.

A karshe dai Mariya Durimin -iya ta ce “A lokacin da kike zawarci, maza za su yi ta zarya a kanki, kowa da irin salon sa da dabarunsa, to, amma ki sani, kashi Casa’in da biyar cikin dari 95% yaudara ce ta kawo su da munanan bukatu. A wannan duniyar ta mu ta yau, ana kallon bazawara a matsayin wacce ruwa ya ci, don haka ba a shakkar ko kunyar gabatar mata da kowace irin bukata, ko mummunar magana”

See also   Gwamnan Akwa Ibom, da Turaki sun ƙalubalanci Rikicin Jahar Benue.

Ta kara da cewa “Soboda haka ki kame kanki ki banbanta kanki da sauran zawarawa, ki san irin mutanen da ya kamata ya ki saurara da irin maganganun da za ki dinga yi da su, kuma ki kaucewa yawan karbar kyauta barkatai don shi ne babban tarkon ‘bata garin samari da Zawarawa”

Sai dai kuma wasu Zawarawa na yin babakere da dukiyar marayun wanda hakan ke jefa yaran da iyayensu cikin matsi na rayuwa da rashin sanin madafa a fannonin da yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here