SANARWA TA MUSAMMAN DAGA RUNDUNAR SOJAN KASAR YEMEN –

0

Nasir Isa Ali
—————–
SANARWA TA MUSAMMAN DAGA RUNDUNAR SOJAN KASAR YEMEN

Yau Ansarullahi ta ragargaji Saudiya.

Mai magana da yawun rundunar Sojan kasar Yemen, Birgediya Janaral Yahya Saree ya bayyana cewar ‘yau rundunar sojan Kasar Yemen,sun samu nasarar kai wasu jerin hare hare kuma cikin wasu dubara da satar numfashin a kan kasar Saudiyar.
Harin ya hada ne da harba masu makaai masu linzami kai tsaye daga Yemen domin janye musu hankali,sannan kuma sai harbi daga jirgin sama mara sa matuki,sai kuma wasu jerin hare haren na daban daga wasu boyayyun wuraren na musamman.

Birgediya Yahaya Saree ya bayyana cewar,wannan sabon harin an kai shi ne domin yin ramuwar gayya a kan Saudiya, wacce ta ke kai wa kasar mu ta Yemen hare hare da jiragen sama tana kashe mana al’umma tare da lalata mata wuraren mu masu muhimmanci,kuma bisa goyon bayan Amurka.

Janaral Saree yace ‘ cikin ikon Allah,yau mun kaddamar da jerin hare hare a kan Saudiya,kuma muna masu sheda muku cewar,mun kai harin ne kan babban birnin makiyan namu,wato birnin Riyadh.
Ofireshin din mai sun “4th Balanced Deterrence Operation” ya fara ne cikin wani lokaci tsararre wanda muka tsara kuma muka aiwatar cikin nasara.

Ina mai sheda muku cewar,hare haren sun rutsa da ma’aikatar Tsaron Saudiya da ma’aikatar Leken asirin Saudiya da kuma filin saukar jiragen sama na “Salman Aii Force Base” Wannan kuwa ya hada ne da Riyadh,yankin Jizan da Najran.
Yahaya Saree ya kara da cewar,mun yi amfani ne da makama masu linzami na QUDUS da ZULFIKQAR

Yahya Saree ya bayyana cewar sun sha jan kunnen Saudiya da kawayenta cewar su daina kai wa Yemen hare hare,kana su janye takunkumi da sauransu daga kan Yemen,ko kuma su ci gaba da fuskantar irin wadannan hare hare din.
A karshe Janar Yahaya Saree ya bayyana cewar lallai Saudiya zata ci gaba da ganin irin wadannan hare hare har sai ita da uwarta Amurka sun dakatar da duk wani ofireshin din dabbancin su a kan Yemen da al’ummarta.

nasirabuhammad@gmail.com
08030750769

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here