FUNTUA ZAMANIN SANATA ABU IBRAHIM

0

FUNTUA ZAMANIN SANATA ABU IBRAHIM

Daga Taskar Labarai

Wani bincike da muka yi da na mu’amala da kuma kai jaje da daukin gaggawa a zamanin sanata Abu Ibrahim tsohon sanatan da ya wakilci Funtua, mun gano abin ya sha bamban tsakanin jiya da yau.

Mun gano abubuwa da yawa amma zamu fadi kadan daga ciki don su zama abin koyi da darasi ga ‘yan siyasar mu.
Lokacin abu Ibrahim na Sanata ‘yan ta’adda suka kai hari a wani gari mai suna Dungun Mu’azu dake a karamar hukumar Sabuwa, sun kashe mutane suka kuma yi barna, kwana daya da ta’addacin sanata Abu Ibrahim yaje garin jami’an tsaro sun gargade shi cewa kar yaje don ko gawarwakin da aka kashe ba a rufe ba kuma ana jin ‘yan ta’addan zasu iya dawowa.

Amma sai da yaje yayi jaje kuma ya basu tallafi yaje Abuja kuma ya tashi ya yi korafin abin da ya faru da koke akan jami’an tsaro basu kai dauki da wuri ba.

A lokacin shi aka kai harin ta’addacin garin Maigora a karamar hukumar Faskari kwana biyu yaje garin ya jajanta ya basu tallafi har ta garmunan shanu masu inji wanda a karon farko da aka fara amfani dasu a jihar Katsina, shima ya tashi gaban majalisa yayi korafi.

A lokacin shi aka tarwatsa wasu kauyukan Kankara a karamar hukumar Kankara. Yaje sansanin ‘yan gudun hijira a Kankara yayi masu magana mai ban tausayi ya kuma basu tallafi.

Anyi wani ambaliyar ruwa a garin Malumfashi yaje ya jajanta ya bada tallafi ya kuma samo gudummuwa daga gwamnatin tarayya ya kawo garin na Malumfashi.

A lokacin shi jaje da barka da ta’aziyya ko yaushe in yazo yankin haka za a rika raka shi yana zuwa amma wani sanatan hatta rasuwa mai dakin Galadiman Katsina mai rasuwa mai shara’a Mamman Nasir ( Allah ya jikansu da Rahama) bai zo ba. Al’ummar na garin Malumfashi suka yi ta sanya ido basu ganshi ba.
________________________________________________!
Taskar labarai na bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma ‘yar uwarta ta Turanci The links news. www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here