DAGA LOKACIN DA NA FARA SANA’AR WAKA ZUWA YAU WAKA 600 NA RERA DA KA

0

DAGA LOKACIN DA NA FARA SANA’AR WAKA ZUWA YAU WAKA 600 NA RERA DA KA— Inji Ado Gwanja

Daga Ibrahim Hamisu

Fitaccen mawakin Hausa kuma wanda yake fitowa a fina-finan Kannywood Ado Gwanja ya ce ya rera kusan wakoki 600 tun da ya soma sana’arsa ta waka kuma galibinsu da ka ya rera su.

Ado Gwanjo ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa Instagram kai tsaye ranar Alhamis.

Da aka tambaye shi ko yin waka yana da wahala, sai ya ce “gaskiya babu abin da yake ba ni wahala” idan ya zo rera waka.
“Ina kiran mai kida na ce ‘buga min kida yanayi kaza, ko yanayi kaza’, sai a yi min kida
sikeleton..

Ado Gwanja ya ce cikin kusan waka dari shida da ya yi, wakoki ba su wuce biyu ba wadanda ya zauna ya rubuta saboda wasu ne suka bashi shawarar yin hakan.

Ado Gwanja ya ce wakar da ya soma yi ita ce Gawasa, wakokinsa da dama sun yi tashe musamman ;Kujerar Tsakar Gida,
Asha Rawa, da Salon Kida.

Mawakin ya ce baya ga sana’ar waka, babu sana’ar da yake so kamar ta shayi.

“Saboda mu asali a gidanmu – ko mace ko namiji, har iyayenmu da sana’ar shayi aka auro su,’ in ji Ado Gwanja.

Wane ne Ado Gwanja?

Dan asalin unguwar Kofar Wambai ce ta Kano,
Mahaifinsa shahararren mai shayi ne da ak fi sani da Gadagi Mai Shayi,
Ya yi karatu har Zuma sakandare,
Yana da mace daya da ‘ya daya
Ya kan fito a fim kuma ya shahara a waka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here