Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Uwargidan sa Farfesa Hafsat Umar Ganduje, da sauran iyalan sa sun kai ziyarar taaziyar rasuwar sirikin su Marigayi tsohon Gwamnan jihar Oyo Alhaji Abiola Ajimobi ga Iyalan sa a gidan su dake Lagos.
Uwargidan marigayin ce ta karbe su, tare da ‘dan ta Idris Ajimobi mijin Fatima Ganduje.
Gwamna ya jagoranci addu’o’in Allah jikan marigayin Ya kuma sa aljannah ce makoma.