LIVERPOOL TA LASHE GASAR PREMIER; BAYAN SHEKARU 30

0

LIVERPOOL TA LASHE GASAR PREMIER; BAYAN SHEKARU 30

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lashe gasar Premier ta Ingila bayan shekaru 30 rabonta da cin gasar.

Hukumar gasar ta bayyana hakan ne bayan kungiyar Chelsea ta lallasa mai biye wa Liverpool din a matsayi na biyu, Manchester City da ci 2-1 a ranar Alhamis

Liverpool ta lashe gasar ne ana saura wasanni bakwai a kammala buga gasar inda ta ba wa City din tazarar maki 23 a saman teburin gasar.

A cikin shekaru 30 Liverpool ta yi mai horaswa guda 9, yayin da ta sayi ‘yan wasa 239, haka kuma ta kashe zunzurutun kudi yuro na kasar Turai biliyan 1 da miliyan 47 duka a yunkurinta na daukar gasar ta Premirer,

A bara dai, kungiyar ta yi kokari sosai wurin neman cin gasar amma Manchester City ta samu nasara a kanta.

Liverpool ta ci wasanni 28 a cikin 31 da ta buga a gasar ta bana, wanda hakan ya sa dan wasanta na gaba Mohammed Salah ya bayyana cewa wannan ce damar kungiyar mafi girma ta lashe gasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here