SHAUKI NE YASA NA AJIYE GURBIN KARATUN PHARMACY NA DAUKI FIM

0
149

SHAUKI NE YASA NA AJIYE GURBIN KARATUN PHARMACY NA DAUKI FIM

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Fitaccen jarumi a masana’rtar Kannywood Ali Nihu ya ce ya ki karbar gurbin katatu a fannin hada magunguna da ya samu a jamia ne, saboda shaukin sa na shaawar yin Fim,

Ali Nuhu ya ce bayan ya kammala sakandire ya rubuta jarabar Jamb, ya kuma ce ya samu gurbin karatu a fannin hada magunguna wato (Pharmacy) a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, amma sai ya ki zuwa yayi karatu saboda burinsa na zama dan Fim,

Jarimi Ali Nuhu ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da wani kamfani samarwa da matasa aikin yi, da bada shawarwari ta shafin sada Zumunta, a hirar ya baiwa matasa tarihin rayuwarsa da irin gwagwarmayar da ya sha domin su amfana da matakan da ya bi ya cimma burinsa.

Jarumin ya ce shaawarsa ga harkar Fim da hazaka da neman sani tare da maida hankali su ne suka sanya ya cimma burinsa na zama babban jarumi a masa’artar Kannywood da ma kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here