AN SAMU KARIN MUTUM BIYAR DA SUKA KAMU DA KURONA A KANO
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Maaikatar lafiya ta jihar Kano sanar da samun mutum 5 masu dauke da cutar Kurona wato Covid-19 daga cikin samfur guda 327 da suka fito a daren Lahadi.
Wannan ta sa adadin wanda suka kamu da cutar a jihar Kano ya zuwa yanzu ya kama mutum 1200 sannan kuma mutum 51 daga ciki sun rasu sannan mutum 866 ne suka warke kuma aka sallamesu gaba daya.