MA’AIKATAN KOTUN DA AKE ZARGIN DA YAUDARAR CIF JOJIN KATSINA:AN GABATAR DA SU KOTU

0

MA’AIKATAN KOTUN DA AKE ZARGIN DA YAUDARAR CIF JOJIN KATSINA:AN GABATAR DA SU KOTU

Daga Abdulmalik Sani

@Taskar Labarai

Kwanakin baya ne labari ya cika kafafen watsa labarai inda aka zargi cewa wasu ma’aikatan kotu da wani lauya sun yaudari babban Jojin jahar Katsina mai shara’a Musa Danladi Abubakar wajen sa hannu ga bada belin wasu manyan masu aikata laifi guda biyu.

A jiya 29/6/2020 jami’an tsaron farin kaya na DSS bayan sun gama bincikensu sun gabatar da mutane hudu a gaban kotu, akan tuhume tuhume-tuhume har guda shidda.

Wadanda ake zargin sune Muhammad Sani Yahaya da Abdullahi Salisu da Aliyu Lawal da Usman D Farouk.
Ana tuhumarsu da zargin farko, cewa sun amshi kudi har naira miliyan hudu daga hannun wata mata da aka sanya wa suna Anti don su taimaka a saki wasu da ake zargi da aikata babban laifi. Masu suna Isiyaku Abubakar da Lawal Abubakar. yan asalin karamar hukumar kankara.

Wadanda ake tsare dasu a gidan yari na Katsina. Zargi da tuhuma ta biyu ga Muhammad Sani Yahaya ya hada baki don samar da wasu takardun karya don a samar da belin wadannan masu laifi da ake tsare dasu.

Zargi na uku ga Aliyu Lawal dake kofar fada garin Kankara, shi ne ake zargi da samar da takardun karya na hakimin Kankara don cika sharuddan belin na karya da aka shirya.

Tuhuma ta hudu Muhammad Sani Yahaya da Abdullahi Salisu da Aliyu Lawal da Usman Farouk. Sun hada baki sun taimaka wajen hada takardun karya da suka kai ga sakin wadanda ake tsare da su.

Tuhuma ta biyar, ana zargin su da su hudun nan sun hada baki suka samar da takardu da hujjojin karya suka yi amfani dasu aka yi kuskuren sakin wasu da ake zargi da satar mutane guda biyu. Wadanda yan asalin karamar hukumar Kankara ne wanda ya sabawa tsarin dokokin kasa.

See also  YADDA BOKANYA TA HALAKA 'YAN FASHIN DAJI DA TSAFI A JIHAR NAIJA

Tuhuma ta shidda Muhammad Sani Yahaya da Abdullahi Salisu da Usman D Farouk. A matsayin su na ma’aikatan gwamnati a wani lokaci cikin watan March. 2020 suka amshi kudi har naira miliyan hudu daga wata mai suna Anti a haramtacciyar hanya.

A jiya an karanta ma wadanda ake zargin tuhume-tuhumen sun musanta duk zarge-zargen da ake masu ba gaskiya bane. Don haka sun karyata abin da ake tuhumar su da shi.

A takardar tuhume-tuhumen da aka baiwa wanda ake zargin wanda Taskar Labarai ta samu kwafi. Ta ga cewa masu gabatar da karar suna da shaidun mutane takwas da suke son gabatarwa.

Uku ma’aikatan kotu ne, biyu mai’aikatan gidan yari, uku jami’an tsaro na farin kaya na Dss. Zasu gabatar da shaidu na takardu guda hudu, daya takardun belin da aka cike biyu takardun masu tsayawa wanda za ai beli na karya da aka cike uku jawabin wadanda ake zargi da suka rubuta bayan an kama su, hudu wasu takardun da aka cike.

A zaman jiya 29/6/2020. An Nemi belin daya daga cikin Wanda ake zargi, amma kotu ta daga sauraren belin sai 9/Yuli/ 2020. An kuma daga ci gaba da zaman shara ar sai 28/Yuli/2020. Kotu ta amince a ci gaba da tsare Wanda ake tuhuma a wajen jami an tsaron Dss.amma ta umurci a kyale Wanda ake zargin su rika ganawa da lauyoyin su.
_______________________________________________
Taskar labarai na bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma ‘yar uwarta ta Turanci mai suna The links da ke www.thelinksnews.com duk suna bisa shafukan sada zumunta na sadarwa.07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here