YAN BINDIGA SUNKAI HARI GARURUWA BIYU, NA BATSARI

0

‘YAN BINDIGA SUNKAI HARI GARURUWA BIYU, NA BATSARI.
@ jaridar taskar labarai
A daren jiya juma’a 03-04-2020, ‘yan bindiga dauke da miyagun makamai sunkai hari Tsugunni da Shirgi wasu kauyuka dake cikin yankin karamar hukumar Batsari.
A Tsugunni sunyi harbe harbe tamkar a fagen daga sun sace shanu da tumaki da suka zarta shittin kuma sun gudu dasu ba tare da samun wata tirjiya ba.

A Shirgi kuma sun kashe wani yaro dan shekara goma biyu (12) wanda ya tsorata ya fito daga gida da gudu da yaji amon bindigun su, sanadin da yasa suka harbe shi. Sannan sunyi ma wata matar aure dukan kawo wuka, sunbi gida gida sun sace shanu da kananan dabbobin garin. Sunyi harbe harbe kamar yadda suka saba kuma sun gudu da dabbobin da suka sata.
________________________________________________
Taskar labarai na a bisa shafin www.taskarlabarai.com yar uwarta ta turancin na bisa www.thelinksnews.com. da sauran shafukan sada zumunta duk sako a aika ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here