HARIN ‘YAN BINDIGA A SALIHAWAR BATSARI ANYI ASARAR RAYUKA.

0

HARIN ‘YAN BINDIGA A SALIHAWAR BATSARI ANYI ASARAR RAYUKA.

Daga Taskar Labarai

Da misalin karfe 11:30pm na daren ranar asabar 04-07-2020 wasu gungun ‘yan bindiga suka kai hari Salihawa dake cikin yankin karamar hukumar Batsari.

Sun bindige mutum biyu Mallam Abdullahi wanda yayi kokarin hanasu tafiya da wata yarinya, dalili ke nan da yasa suka yi mashi harbi biyu, take yace ga garinku nan, sai Sabe Abubakar wanda suka harba a kafa ya rarrafa ya shiga gida suka bishi suka kara mashi harbin da yayi sanadiyyar mutuwar shi.

Sun yi harbe-harbe wanda ya razana mazauna garin Batsari sosai domin kowa ya dimauce yadda ake jin rugugin bindugu na tashi kamar a filin fama, sanna kowa ya dauka cikin garin abun ke faruwa. Bayan sun bi gidajen mutane sun sace kudi da wayonyin hannu, kuma sun tattaro shanu, tumaki da awaki, suna kokarin tafiya, sai jami’an tsaro suka rutsa dasu aka yi ta masayar wuta, daga baya suka gudu amma ana zaton an kashe wasu daga cikin su.

Haka kuma ana zaton ‘yan bindigar sun harbi soja daya a kafa, kodayake mun yi kokarin jin tabakin jami’an tsaro amma abun ya ci tura.

Da gari ya waye an gano wani daga cikin barayin ya fake cikin wani rogo cikin jini sakamakon harbin da jami’an tsaro suka yi masa, anyi mashi tambayoyi ya bayyana cewa gayyato shi aka yi, wasu fulani dake kusa da Salihawa; Jamilu da Kabir Maidawa ne suka gayyato su domin su kawo harin, daga bisani bayan ya gama bada bayanai sai rai yayi halin shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here