GWAMNA GANDUJE YA JAGORANCIN ZAMAN FARKO NA YAKIN NEMAN ZABEN EDO

0
206

GWAMNA GANDUJE YA JAGORANCIN ZAMAN FARKO NA YAKIN NEMAN ZABEN EDO

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci zaman farko na kwamitin yakin neman zaben jihar Edo wanda yake shugabanta, bayan an kaddamar da su a jiya a hedikwatar jam’iyar APC na kasa.

Taron Wanda shi ne na farko ya samu halartar Gwamnonin Kogi, da Lagos da Gombe, da kuma tsofaffin gwamnonin Edo, Abia da Ananbra,

Haka kuma taron ya samu halartar sanatoci, yan majalisar taraiya, ministoci da sauran membobin kwamitin.

An dai gudanar da taron ne dai a masaukin Gwamnan Kano wato Mallam Aminu Kano Lodge dake Asokoro da ke birnin Abuja.

Gwamna Ganduje na tare da Sanata Barau Jibrin, Shugaban jam’iyar APC na jiha Hon Abdullahi Abbas, da tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here