HUKUMAR KASHE GOBARA TA CETO RAYUKA 430 A JIHAR KANO

0

HUKUMAR KASHE GOBARA TA CETO RAYUKA 430 A JIHAR KANO

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta samu damar ceto rayuka 430 tare da dukiya ta naira miliyan dubu 3 a ibtilain gobara da aka samu a wurare daban daban daga watan Janairun zuwa Yunin da ya gabata,

Kakakin hukumar Saidu Muhammad shi ne ya bayyana haka ga manena labarai yana mai cewa akasarin gobar ta faru ne a lokacin zaman kulli da gwamnatin kano ta sanya domin dakile Annobar Kurona.

Malam Saidu ya kara da cewa rayuka 74 ne suka salwanta, tare da kadarori na sama da naira miliyan 535 a cikin wannan tsuki, sannan kuma sun karbi kiraye kiraye guda 496 a sassa daban-daban na jihar nan, kuma guda dari 260 na neman dauki ne, yayin da guda dari suka kasance na gangan,

Kakakin hukumar gobar ya jaddada cewa mafiya akasarin gobarar ya faru ne sanadiyar wutar lantanki, yana mai shawartar jama’a da su kasance masu yin taka tsantsan a lokacin da suke amfani da kayan wutar lantanki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here