YAN NAGERIYA 246 AKA KILLACE BAYAN DAWOWARSU DAGA DUBAI

0

‘YAN NAGERIYA 246 AKA KILLACE BAYAN DAWOWARSU DAGA DUBAI

Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare ta ce, an dawo da mutane 246 daga haaddiyar daular Larabawa watau Dubai.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar jiya a Abuja,

A cewar hukumar, an dawo da su gida ne bayan da annobar COVID-19 ta sanya su suka makale a can na tsawon lokaci.

Jiya Laraba ne dai jirgin da ya yo jigilar mutanen ya sauke su a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos.

Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa dama tun gabanin kwaso sun an cimma natsaya kan
cewa za a killace mutanen har na tsawon makonni 2 a wani mataki na tabbatar da lafiyarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here