BARAYIN DAJI SUN KAI HARI KAUYEN DAN GEZA

0

BARAYIN DAJI SUN KAI HARI KAUYEN DAN GEZA
@ taskar labarai
Yanzu da yammacin lahadi ‘yan bindiga su biyu kan babur suka shiga kauyen Dan geza dake cikin yankin karamar hukumar Batsari
Da shigar su , suka kama harbin mutane kan mai uwa da wabi. Ya zuwa yanzu sun harbi mutum ukku ciki hadda wani karamin yaro da harsashe ya tarwatsa masa yatsan kafa .
Da wasu matasa guda biyu wadanda suka samu suka iso Batsari ba shiri. Amma dai bamu iya tantance adadin wadanda suka harba ba sai kura ta nutsa.
Hade da Dan rahoton nan ga hotunan wadanda aka harba.@ taskar labarai. Www.taskarlabarai.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here