GANDUJE YA SHIRYA WALIMAR CIN ABINCI GA ‘DAN MINISTAN SHAIRI’A

0

GANDUJE YA SHIRYA WALIMAR CIN ABINCI GA ‘DAN MINISTAN SHAIRI’A

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya shirya liyafar cin abinci ga Ministan Shari’a na ƙasa Abubakar Malami wadda aka daura auren ‘dan sa yau a Kano,

Taron liyafar cin abincin ya samu halatar manyan baki da suka hada da Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, da na jihar Kebbi Atiku Bagudu sai kuma na Zamfara Bello Matawallen Muradun da takwaransa na Jigawa Muhammad Badaru Abubakar.

Sauran manyan bakin sun hada da Mele kyari manajan darakta na NNPC da manajan darakta na kamfanin rarraba hasken wutar lantarki wato TCN da ministan ma’aikatar wutar lantarki da sauransu.

See also  Zuwan Mu Wajen Buhari Barka Da Sallah tare da Danlami kurfi.

A yau ne dai aka daura auren Abdulaziz Abubakar Malami da amaryarsa Khadija Abduljalil Dambatta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here