MAN CITY TA YI NASARAR DAUKAKA KARA A KAN BUGA GASAR ZAKARUN TURAI

0

MAN CITY TA YI NASARAR DAUKAKA KARA A KAN BUGA GASAR ZAKARUN TURAI

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Daukaka kara da kungiyar Manchester City ta yi na haramta mata shiga gasar zakarun turai tsawon shekara biyu ya yi nasara, kuma za su taka leda a duk wata gasar Turai a kakar wasa mai zuwa. Sannan kuma an rage tarar da aka ci kungiyar daga Euro miliyan 30 zuwa Euro miliyan 10.

Hukumar kula da harkokin kudi ta UEFA ta ba da sanarwar dakatar da kungiyar a watan Fabrairu saboda “keta haddi” gami da harkokin kudi tsakanin 2012 zuwa 2006.

Kulob din Premier ya nuna rashin amincewarsa da wannan laifi sannan ya daukaka kara kan hukuncin a CAS a watan da ya gabata, bayan da a baya aka bayyana matakin ladabtar da UEFA a matsayin “wariya.”

See also  AN HARAMTA KAMA KARUWAI A NAJERIYA

Bayan jin hujjoji na tsawon kwanaki uku a watan Yuni, CAS ta soke dakatarwar ma’ana City na da ‘yancin yin wasa a gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa, bayan da ta take matsayi na biyu a teburin Premier bayan da ta lallasa Brighton 5-0 ranar Asabar da ta gabata.

Da yake magana bayan wasan, Kocin City Pep Guardiola ya ce yana da yakinin cewa za a soke haramcin kuma ya ce kungiyarsa ta cancanci taka rawa a gasar manyan kungiyoyin kwallon kafa ta Turai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here