KEDCO TA RASA MA’AIKATANTA GUDA BIYU

0

KEDCO TA RASA MA’AIKATANTA GUDA BIYU

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Kamfanin rarraba wutar lantar na KEDCO ya sanar da mutuwar Ma’aikatansa biyu sakamakon hatsarin mota a jihar Katsina.

Mai magana da yawun kamfanin Ibrahim Sani Shawai ya bayyana cewa, Malam Nasir Ahmad da Malam Abdulra’uf Ahmad sun rasa rayukansu a hanyar su ta dawowa Kano daga jahar Katsina daga wani aiki na musamman.

Ya ce hatsarin ya afku ne a karamar hukumar Kankiya da ke Jihar Katsina wanda mota kirarar Bus mai lamba ( KMC366AA) ta shigo musu.

Sauran mambobin tafiyar shida duk sun sami rauni ka, sai dai direban na su mai suna Mr Johnson bai sami rauni ko kadan ba.

See also  BARAKA A TSAKANIN LADO DA MAJIGIRI

Haka kuma duk Ma’aikatan nasu da sukaji rauni sun dauko su zuwa Kano.

Iyalan daya daga cikin mutane biyun da suka rasa ransu Malam Abdulra’uf Ahmad sun ce za’ayi jana’idarsa a Dandalin- Fagge Maikwaru Avenue, ranar talata a karamar hukumar Fagge da ke jahar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here