MASARAUTAR KANO TA HANA GUJE-GUJE DA DAWAKAI

0

MASARAUTAR KANO TA HANA GUJE-GUJE DA DAWAKAI

Daga Ibrahom Hamisu, Kano

Majalisar masarautar Kano ta sanar hana guge-guje da dawakai a cikin gari da wasu daga cikin matasa ke yi da sunan atisaye.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da masarautar ta fitar yau Litinin mai ɗauke da sa hannun Turakin Kano kuma shugaban Kwamitin hawan dawakai na masarautar Alhaji Lamido Abdullahi Sanusi.

Sanarwar ta ruwaito cewa an ɗauki matakin ne biyo bayan koke-koke masu yawa da mai martaba sarkin Kano yake samu game da haye-hayen dawakai barkatai marasa
dalili da sukwane-sukwanen ‘yan Atisaye da ke jawo buge kananan yara da
mata musamman wadanda suka manyanta da kuma ta’addancin bata-gari dake jawo asarar dukiyar al’umma.

Haka Kuma sanarwar ta ce, gabanin daukar matakin sai da mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya umarci kwamitin na Durbar da ya yi bincike da neman shawarwari tare da tattaunawa da Kwararrun masana harkokin tsaro da Gwamnati wanda ita ma abin ya dameta don a samu matakan da yakamata a dauka.

Matakan da masarautar ta dauka sun haɗar da soke hawan Atisaye baki ɗaya da dakatar da Hawan Angwanci har sai an fito da tsare-tsare masu kyau da nagarta, sannan Kilisa ta al’ada don motsa Dawakai ba’a yarda a yi ta ba sama da dawakai uku zuwa biyar, Kuma lalle wandanda za su hau kilisar su kasance a cikin kyakkyawar shiga ta kamala Kuma ba’a yarda su yi sukuwa a inda bai kamata ba, kamar lunguna.

Kakaki24 ta ruwaito sanarwar ta yi kira ga jama’a da su kiyaye da ka’idar, kuma za a hukunta duk wanda ya karya dokar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here