Kano: Majalisa ta amince da hukuncin fiɗiye ga masu fyaɗe

0

Kano: Majalisa ta amince da hukuncin fiɗiye ga masu fyaɗe

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Majalisar dokoki ta jihar Kano za ta gyara dokar hukunta masu aikata laifukan fyade ta shekarar 2014 daga ɗaurin shekaru 14 zuwa fiɗiye.

Amincewa da hukuncin ya biyo bayan ƙudurin da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Rano Nuraddeen Alhassan ya gabatar a zaman ta na jiya Laraba 15 ga watan Yuli.

Shafin Daily Nigerian ya ruwaito cewa yayin gabatar da ƙudurin dai, Nuraddeen Alhassan ya ce, gabatar da ƙudurin nasa ya biyo bayan yawaitar samun rahotonnin yin aikata fyade a wannan lokaci don haka akwai buƙatar majalisa ta gyara dokar kasacewar hukuncin na baya ya yi kaɗan.

Yayin zaman ɗan majalisa na Tarauni Lawan Rabi’u, ya buƙaci a sauya hukuncin ya koma ɗaurin rai da rai maimakon fiɗiye, yana mai cewa Hakan zai fi hukuta masu aikata laifin.
Bayan tafka muhawara ne kuma mambobin majalisar suka amince da hukuncin na fiɗiye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here