AN DAKATAR DA TSOHON SHUGABAN JAM ‘YYAR APC NA MASHI DAGA JAM’IYAR

0

AN DAKATAR DA TSOHON SHUGABAN JAM ‘YYAR APC NA MASHI DAGA JAM’IYAR

@Taskar Labarai

Jam’iyyar APC a matakin karamar hukuma ta dakatar da tsohon shugaban jam’iyyar arma ya u Bala Doka daga jam’iyyar takardar wadda shugaban jam iyyar na mashi Alhaji sanusi muntari doguru .ya sanyawa hannu. Tare da shugabannin jam iyyar su ashirin da hudu a mataimakin karamar hukuma da unguwanni.
Dakatarwar ta taso ne daga matakin unguwar sa.

Wadanda suka yi taro suka dakatar da shi, bisa zargin zagon kasa da bata sunan wasu manyan ‘yan jam’iyyar dake Mashi.
Takardar dakatarwar ta samu amincewa da sanya hannu duk shugabannin jam’iyyar na karamar hukumar Mashi.

Sakon dakatarwar har sun isar da shi ga uwar jam’iyya ta jiha kamar yadda tsarin mulkin jam’iyyar ya tana da.

Shi tsohon shugaban armaya u balq doka shi ne wanda ya kira taron manema labarai a Katsina, inda ya shelanta cewa, zai jagoranci yin kiranye ga dan majalisar tarayya mai wakiltar Mashi da Dutsi Alhaji Mansir Ali Mashi akan wata murya da aka ji kuma ake zargin tashi ce, tana suka ga akan yadda shugaban kasa Buhari yake tafiyar da wasu harkokin mulkin kasar nan.

Muryar da Dan majalisar tarayya ya kai korafi akan ta ga jami’an tsaro yana neman a yi bincike.
Har zuwa rubuta rahoton nan, jam’iyyar APC a matakin karamar hukuma bata yi magana akan muryar ba ko dan majalisar da ake zargi tasa ce.

Da wannnan dakatarwar ta armayau bala Doka yanzu ya tashi da zama dan jam’iyyar har sai uwar jam’iyyar ta jiha ta dau matsaya akan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here