ANYI GARKUWA DA ‘YAR DAN MAJALISAR JIHAR KANO
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun afka gidan dan majalisar jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Danbatta Hon. Murtala Isah Kore inda suka yi garkuwa da yarsa
Al’amarin dai yafaru ne Adaren jiya, bayan da Masu Garkuwar suka shiga gidan Kuma sun Iske Baya nan gidan shi ne suka suka yi Garkuwa da yarsa mai kimanin shekaru 17.
An tuntubi shugaban Karamar Hukumar ta Danbatta Idris Haruna zago ya tabbatar da wannan Labarin,
Yayin da ita ma rundunar yan sanda ta jihar kano ta ce zata Bincka domin Bayyana wa manema labarai matsayinsu.