INA LAIFIN IBRAHIM MAGU? (1)
Daga Farfesa Ibrahim Malumfashi
Ya zuwa yanzu na san muna da labarin halin da Ibrahim Magu, tsohon Shugaban Hukumar EFCC yake ciki, musamman yadda yake zaune gaban wata hukumar tana binciken shi domin badakalar kudade da gidaje da sauran kadarori da ake tuhumarsa da su. Ibrahim Magu ne fa saboda rashin iya aikinsa, ‘yan majalisar kasa suka ce ba za su amince a sake nada shi kan mukamin ba, domin ba su yarda da gaskiyarsa ba, amma Shugaba Buhari ya yi mirsisi ya ce ai ba wanda ya iya kamo barayi irin sa, ya ce dole a sake nada shi, ko kuma ya ci gaba da gudanar da aikinsa haka. Shi din ne dai yanzu ake zargi da sata da almundahaa da wawurar dukiyar al’umma da makamantan haka daga gwamnatin Buhari mai gaskiya!
Ga wadanda suka nakalci yanayin sata da cin hanci da rashawa irin ta Nijeriya, wannan ba zai zama da mamaki ba, domin mun san za a kai ga wannan matsayi wata rana, wato inda ko dai mai dokar barci ya shiga gyangyadi ko kuma sata ta saci satar ko wani abu mai kama da haka. Ba kuma wani abu ya sa haka ba, sai ganin cewa, sata da cin hannci da rashawa sun samu wurin zama a kasar nan, sun kuma hakince da ba sai an je nemo su ba.
Ga masu tunani irin nawa, mun dade muna fadar cewa ba wani abu ne ya addabi kasar ba, face shegiyar sata da wasu daga cikin al’ummar kasar ke faman yi, amma su kare ba wanda ya san inda suke ko kuma yadda suka yi da dukiyar jama’a da suka sace, saboda barayin da kayan satar sun nashe a cikin kasa ta yadda ba a gane masu yi ko yadda aka yi da dukiyar da aka sace.
Idan ka tashi kana neman sanin inda wadannan barayi suka shige, bayan sun yi satar, sai ka ji gum, in an taso ana bincike kamar a kame a daure, sai ka gai abin duk tashin gishirin andirus ne, an fado kasa ba nauyi. A lokutta da dama, sai abin ya zama tamkar sihiri in ana neman barayin kasar, ga su ana maganar su, amma ba a ganin su.
Kullum abin da muke bukata shi ne mu gan su, ba don wani abu ba sai don in har ba a iya kame su, a hukunta, to mu san mazauninsu da yadda in mun gan su za mu gane su, mu kyamace su, a kauce musu, a kuma nemi Allah ya yi doguwar katanga tsakaninmu da su. Sai dai ba wani abin tada hankali irin ko-in-kula- da ake yi wa wannan matsala ta sata da barna a cikin kasar, ta yadda sai a kasa gane wane ne barawon, wane ne ke neman kama barawon, wa kuma ke bin sawun barawon da wanda ke neman kama mabi sawun barawon ko mai neman kamawar. Abin sai ka ga tamkar yanar gizo da kuda ya fada ciki ne, duk yadda yake so ya fita, sai kara daure kansa yake a ciki.
To amma da alama mun fara samun haske yanzu da aka soma tuhumar irin su Ibrahim Magu, tsohon Shugaban EFCC da wasu irin sa, sai dai ai ba yanzu aka fara ba, domin ko a watanni baya wasu daga cikin mu sun fara bayyana mana ko su wane ne barayin kasar nan, sun kuma bayyana mana inda za mu je mu gan su ko mu nema su in da gaske muke yi, banza kurum muka yi da su! Daya daga cikin jiga-jigan siyasa da mulkin kasar ne, wato Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a zamanin Jamhuriyya ta biyu, a karkashin jam’iyyar PRP ta Malam Aminu Kano, ya taba fasa kwai game da barayin kasar nan, wadanda suke neman sai sun durkusar da ita.
Amma me muka yi a lokacin?
Me Alhaji Balarabe Musa ya ce a lokacin? Kai tsaye ya yi, domin kuwa cewa ya yi ‘matsalar da muke ciki a kasar nan ita ce, shugabanninmu a cikin kasar BARAYI ne kurum.’ Ya kara da cewa ‘idan har abin da na fada akwai tababa, bari na sake tuna mana, duk wani wanda ya samu dama ya zama Kansila ko Mamba na Majalisar Jiha ko Sanata ko Gwamna ko Shugaban kasa to ba talakawa ya yi ko zai yi wa aiki ba, kansa ya bauta wa, ko yake bauta wa, shi ya sa nan da nan za a ga ya fi kowa kudi daga yankin da ya fito. Kansila a yawancin wurare ya fi kowa arziki a mazabarsa. Shugaban kasa da ya bar mulki, shi za ka ga ya fi kowa wandaka da dukiya a cikin kasar, ko da kuwa kafin ya hau karaga, mahaifinsa ba kowan kowa ba ne.”
Da yake kwatanta shugabannin da da na yanzu, Alhaji Balarabe Musa ya ce ai bai dace a auna ko kwatanta ba. Ya yi tambayar da a nuna masa dukiyar da su Azikiwe ko Awolowo ko Sardauna ko Aminu Kano suka bari bayan sun sauka daga mulki, babu, domin su ba sata suka shiga siyasa ko hawan mulki su yi ba, sun bauta wa jama’a da kasarsu ne bisa amana da yarda. Amma shugabannin yanzu, tun tashin farko, ba su da tunanin al’umma ko kasa a ransu, abin da suka fi damuwa shi ne, su kwashe dukiyar al’umma su kai cikin bankunan cikin gida da kasashen waje su kimshe, su bar jama’a cikin kunci da talauci da damuwa.
Wannan fitar kutsu da Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya yi game da bayyana wadanda suka takaita kasar nan da yadda suka takaita ta din da kuma ko su wane ne su, shi ne abin farin cikina a wancan lokaci, amma me aka yi da wannan hasashe?.