SOJA SUN FAFATA DA YAN BINDIGA A JIBIA

0

SOJA SUN FAFATA DA YAN BINDIGA A JIBIA
@ jaridar taskar labarai
Wata majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa.sojan Najeriya sunyi mummunar fafatawa da wasu yan bindigar daji masu dauke da Muggan makamai.a karamar hukumar jibia ta jahar katsina
Majiyarmu tace sojan sun samu bayanin wasu barayi ne a yankin shimfida wajen tsamben tsauni.inda suka isa wajen suka kuma yi masu barna sosai.
Majiyarmu tace, akan hanyarsu ta dawowa.sai yan bindigar sukayi masu kwantar bauna.majiyarmu ta tabbatar da anyi ma sojan mugun barna.wanda har zuwa rubuta labarin nan ba a iya tantancewa ba.
Amma jaridar nan ta tabbatar da cewa, an kai wasu sojan da aka Jima ciwo a babban asibitin gwamnatin tarayya dake katsina.
Jaridar nan ta kasa samun tabbacin sun kai su nawa.wani soja ya tabbatar mana da anyi masu kwantar bauna kuma anyi masu barna.
Majiyarmu ta tabbatar da cewa sojan sun sake shiri inda suka koma sun kuma kashe yan bindigar masu yawan gaske. Sun kwashe baburan su.
Yankin shimfida a karamar hukumar jibia yana hannun babban Dan bindiga nan ne da ake Kira dangote.wata majiya a cikin fulanin ta tabbatar mana da cewa yaran Dangote ne suka kai wannan harin.kuma tabbas sunyi ma soja barna,
suma an masu mummunar barna.
_____________________________________________
Taskar labarai tana a bisa shafin www.taskarlabarai.com da kuma yar uwarta ta turanci mai suna The links news dake a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. Duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here